Majalisar Dattawan ta yi tir da wata zanga-zanga da aka yi a Ghana, inda wasu ke buƙatar a kori ’yan Nijeriya daga ƙasar.
Shugaban kwamitin majalisar kan ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, Sanata Bassey Aniekan, ya ce ba daidai ba ne a zargi dukkan ’yan Nijeriya saboda laifin wasu ƙalilan.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
- Zaɓen 2027: Arewa Za Ta Sake Mara Wa Tinubu Baya — Gwamna Inuwa
Ya ce ’yan Nijeriya mutane ne masu zaman lafiya, masu aiki tuƙuru, kuma suna taka rawar gani a ƙasashen da suke ciki, ciki har da Ghana.
Sanatan ya buƙaci ’yan Ghana da su tuna alaƙa ta tarihi, tattalin arziƙi da al’adu da ke tsakanin Nijeriya da Ghana.
Ya kuma shawarci ’yan Nijeriya da ke Ghana da su kwantar da hankali, kada su ɗauki fansa, yana mai tabbatar musu cewa gwamnatin Nijeriya na tattaunawa da hukumomin Ghana domin magance matsalar cikin lumana.
Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar.
Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su ne ci gaba da zama ginshikin dangantakar ƙasashenmu biyu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp