Majalisar dokokin jihar Taraba, ta yi kira ga hukumomin tarayya da na jihohi da su ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a jihar, sakamakon kashe-kashen da aka yi a baya-bayan nan na rashin hankali da lalata dukiyoyi.Â
A wani kudiri da wasu mambobin majalisar suka gabatar a ranar Laraba; Hon. Abubakar John Tanko, Takum (1), Hon. John Lamba, Takum (II), Hon. Joshua Urenyang, Ussa, Hon. Angye Josiah Yaro, Wukari (II), Hon. Jethro Yakubu, Wukari (I) da Hon. Annas Shuaibu – Karim-Lamido (II), sun bukaci gwamnati da ta gaggauta shawo kan matsalar tsaro a mazabun jihar daban-daban.
Kudirin hadin guiwar wanda Hon. Tanko na Takum (I) ya bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hare-hare a kauyuka da dama a sassan Kudancin Taraba da kuma karamar hukumar Karim-Lamido ta jihar.
A cikin kudirin, ‘yan majalisar sun kara da cewa, hare-haren wuce gona da iri da ake kai wa a mazabunsu na janyo asarar rayuka da dukiyoyi da suka hada da gonaki da sauran hanyoyin rayuwa na al’ummar mazabar.