Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 437.3.
Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kudi na majalisar ya yi a zaman majalisar da ya gabata a Laraba.
- INEC Za Ta Gudanar Da Zaɓuɓɓuka 34 Cikin Fabrairun 2024 – Yakubu
- Akpabio Ya Rantsar Da Lalong A Matsayin Sanata Mai Wakiltar Filato Ta Kudu
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa kasafin kudin ya bi karatu uku kafin majalisar ta zartar da shi.
Shugaban majalisar ya umarci magatakardar majalisar, da ya gabatar da kwafin kasafin kudin shekarar 2024 domin mika wa Gwamna Abba Yusuf gaba domin amincewarsa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini (NNPP-Dala) ya shaida wa NAN jim kadan bayan kammala zaman majalisar cewa kasafin zai saukaka ayyukan raya kasa da dama domin amfanin jihar.
“A cikin kasafin kudin, an ware kashi 67 bisa 100 na manyan ayyuka, yayin da kashi 33 na kudaden da ake kashewa akai-akai.”
Ya ce ilimi ya samu kaso 30 cikin dari sai kuma kiwon lafiya da ababen more rayuwa.
NAN ta ruwaito cewa Gwamna Abba a ranar 27 ga watan Oktoba ya gabatar da kasafin kudin ga majalisar domin amincewa.