Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta warware dukkan basussukan da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ke binta wanda ya kai naira miliyan 109.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a yayin zamanta na ranar Laraba wanda shugaban majalisar Alhaji Hamisu Chidari ya jagoranta bayan gabatar da rahoton kwamitin matasa da wasanni na majalisar.
Majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki koma bayan da kungiyar kwallon kafar ta samu na fita daga kungiyar kwararrun kwallon kafa ta Nijeriya.
Da yake gabatar da rahoton kwamitin, shugaban kwamitin matasa da wasanni na majalisar, Alhaji Nuradeen Ahmad, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta rika biyan bashin kungiyar acikin kowane wata.
“Majalissar ta yi kira ga mahukuntan kungiyar Kano Pillars da masu ruwa da tsaki a jihar da su hada kai su kara taka tsantsan wajen tafiyar da kudaden shigar da suke samu, don kada su dogara da gwamnatin jihar kadai.
“Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gyara filin wasa na Kano Pillars domin gudanar da wasanni da sauran gasa.
“Majalissar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da ofisoshi na dindindin da sansanonin gudanar da kungiyar tare da daukar kwararrun ’yan wasa da masu horarwa ba tare da siyasanci ba a lokacin daukar ‘yan wasan da masu horaswa.