Majalisar dokokin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, ta yi fatali da ƙudirin gyaran haraji da ke gaban majalisar tarayya. Shugaban masu rinjaye, Lawan Husseini, ya gabatar da ƙudirin a matsayin “muhimmin batu na gaggawa,” yana mai cewa ƙudirin zai cutar da jihohin Arewa idan aka amince da shi.
Husseini ya ce tsarin rarraba harajin VAT a ƙudirin ba ya da adalci, saboda jihar Legas ce za ta fi amfana sakamakon kasancewar shalƙwatar manyan kamfanoni da bankuna na jihar. Ya ce, “Kashi 80 cikin 100 na kudin VAT zai shiga Legas, yayin da jihohin Arewa za su samu kaso kaɗan, wanda zai kara talauci da rashin biyan albashi.”
- Gwamnati Ta Karyata Shirin Karin Harajin VAT
- Harajin “VAT” Zai Kara Wa Al’ummar Kasar Nan Kuncin Rayuwa Ne Kawai – Gambo Danpass
‘Yan majalisa, ciki har da Hon. Salisu Mohammed da Hon. Murtala Kadage, sun yi kira ga Majalisar Dattawa da ta fi mai da hankali kan batutuwan tsaro da rashin aikin yi maimakon saurin amincewa da ƙudirin. Sun buƙaci wakilan Arewa da su haɗa kai don hana ƙudirin ganin hasken rana don kare muradun yankin.