Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta tsige mataimakin shugaban majalisar kuma mamba mai wakiltar mazabar Ankpa ta Daya, Hon. Ahmed Muhammed daga mukaminsa.
A zaman gaggawa da ta gudanar a ranar Juma’a a birnin Lokoja, mambobin majalisar sun zargi Hon Ahmed Muhammed da sauran shugabannin majalisar guda uku da rashin nuna da’a da kuma yin amfani da ofisoshinsu ba bisa ka’ida ba.
- 2023: Muna tattaunawa da Peter Obi kan yiwuwar hada takararmu — KwankwasoÂ
- ‘El-Rufa’i Ya Cancanci Yabo Wajen Gudanar Da Ayyukan Ci Gaba’
Wani kudurin gaggawa da ya gabatar a zauren majalisar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Dekina/Okura, Hon Enema Paul, ya ce ‘yan majalisar 17 cikin 25 da ke majalisar ne suka sanya hannun amincewa da tsige Hon Ahmed Muhammed da kuma dakatar da sauran shugabannin uku.
Shugabannin uku da aka dakatar daga majalisar da aka raba su da mukamansu, sun hada da Hon Bello Hassan Balogun (Shugaban masu rinjaye) da Hon Idris Ndako (Mataimakin masu rinjaye) da kuma Hon Edoko Moses Ododo (Mai tsawatarwa).
Kazalika, majalisar ta sanar da sunan Hon Alfa Momoh Rabi’u mai wakiltar mazabar Ankpa ta Biyu, a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.
Sauran shugabannin majalisar da aka zaba sun hada da Hon Muktar Bajeh, a matsayin sabon shugaban masu rinjaye da Hon Umar Isah Tanimu wanda shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye da Hon Ahmed Dahiru, a matsayin mai tsawatarwa na majalisar da kuma Hon Enema Paul, wanda zai kasance sabon mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dokokin ta Jihar Kogi.
Tun da farko sai da shugaban majalisar, Hon Mathew Kolawole ya sanar da rushe dukkan kwamitocin majalisar.
An dai samar da kwararren matakan tsaro a harabar majalisar a yayin zaman.
‘Yan majalisa 17 cikin 25 ne suka halarci zaman majalisar na ranar Juma’a.