• Leadership Hausa
Friday, August 12, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Siyasa

Majalisar Dokokin Kogi Ta Tsige Mataimakin Kakakin Majalisar, Ta Dakatar Da wasu 3

by Ahmed Muhammed Danasabe
2 months ago
in Siyasa
0
Majalisar Dokokin Kogi Ta Tsige Mataimakin Kakakin Majalisar, Ta Dakatar Da wasu 3
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta tsige mataimakin shugaban majalisar kuma mamba mai wakiltar mazabar Ankpa ta Daya, Hon. Ahmed Muhammed daga mukaminsa.

A zaman gaggawa da ta gudanar a ranar Juma’a a birnin Lokoja, mambobin majalisar sun zargi Hon Ahmed Muhammed da sauran shugabannin majalisar guda uku da rashin nuna da’a da kuma yin amfani da ofisoshinsu ba bisa ka’ida ba.

  • 2023: Muna tattaunawa da Peter Obi kan yiwuwar hada takararmu — Kwankwaso 
  • ‘El-Rufa’i Ya Cancanci Yabo Wajen Gudanar Da Ayyukan Ci Gaba’

Wani kudurin gaggawa da ya gabatar a zauren majalisar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Dekina/Okura, Hon Enema Paul, ya ce ‘yan majalisar 17 cikin 25 da ke majalisar ne suka sanya hannun amincewa da tsige Hon Ahmed Muhammed da kuma dakatar da sauran shugabannin uku.

Shugabannin uku da aka dakatar daga majalisar da aka raba su da mukamansu, sun hada da Hon Bello Hassan Balogun (Shugaban masu rinjaye) da Hon Idris Ndako (Mataimakin masu rinjaye) da kuma Hon Edoko Moses Ododo (Mai tsawatarwa).

Kazalika, majalisar ta sanar da sunan Hon Alfa Momoh Rabi’u mai wakiltar mazabar Ankpa ta Biyu, a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.

Labarai Masu Nasaba

Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP

Gwamna Wike Ya Karyata Batun Maka Atiku Da Tambuwal A Kotu

Sauran shugabannin majalisar da aka zaba sun hada da Hon Muktar Bajeh, a matsayin sabon shugaban masu rinjaye da Hon Umar Isah Tanimu wanda shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye da Hon Ahmed Dahiru, a matsayin mai tsawatarwa na majalisar da kuma Hon Enema Paul, wanda zai kasance sabon mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dokokin ta Jihar Kogi.

Tun da farko sai da shugaban majalisar, Hon Mathew Kolawole ya sanar da rushe dukkan kwamitocin majalisar.

An dai samar da kwararren matakan tsaro a harabar majalisar a yayin zaman.

‘Yan majalisa 17 cikin 25 ne suka halarci zaman majalisar na ranar Juma’a.

Tags: HukunciMajalisar Dokokin Jihar KogiMataimakin Kakakin MajalisarSiyasaTsigewaZaman Gaggawa
ShareTweetSendShare
Previous Post

2023: Muna Tattaunawa Da Peter Obi Kan Yiwuwar Hada Takararmu — Kwankwaso 

Next Post

Zulum Ya Amince Da Daukar Likitoci 40 Aiki Don Tura su Karkara

Related

Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP
Siyasa

Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP

7 hours ago
Gwamna Wike Ya Karyata Batun Maka Atiku Da Tambuwal A Kotu
Siyasa

Gwamna Wike Ya Karyata Batun Maka Atiku Da Tambuwal A Kotu

8 hours ago
Gwamna Wike Ya Karyata Cire Tutocin PDP Daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas
Siyasa

Gwamna Wike Ya Karyata Cire Tutocin PDP Daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas

9 hours ago
Zaben Fidda Gwanin PDP: Wike Ya Gurfanar Da Atiku, Tambuwal Da INEC A Gaban Kotu
Siyasa

Zaben Fidda Gwanin PDP: Wike Ya Gurfanar Da Atiku, Tambuwal Da INEC A Gaban Kotu

10 hours ago
Dariye Zai Tsaya Takarar Sanata A Filato Bayan Yi Masa Afuwa Daga Gidan Yari
Siyasa

Dariye Zai Tsaya Takarar Sanata A Filato Bayan Yi Masa Afuwa Daga Gidan Yari

1 day ago
Jerin Sunayen Sabbin Ministocin Da Buhari Ya Aike Wa Majalisar Dattijai Ta Tantance Su
Siyasa

DA DUMI-DUMI: Buhari Ya Gana Da Iyalan Fasinjojin Jirgin Da Aka Sace A Kaduna

1 day ago
Next Post
Zulum Ya Amince Da Daukar Likitoci 40 Aiki Don Tura su Karkara

Zulum Ya Amince Da Daukar Likitoci 40 Aiki Don Tura su Karkara

LABARAI MASU NASABA

Da Dumi-Dumi: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai 

Rashin Tsaro Na Kawo Koma Baya Ga Tattalin Arzikin Nijeriya – Buhari

August 12, 2022
Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

August 12, 2022
Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya

Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya

August 12, 2022
Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

August 12, 2022
Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

August 12, 2022
Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

August 12, 2022
Hisbah Ta Jadadda Muhimmancin Gwajin Lafiya Kafin Aure 

Hisbah Ta Jadadda Muhimmancin Gwajin Lafiya Kafin Aure 

August 12, 2022
Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai

Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai

August 12, 2022
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 2.6 Domin Tsaron Abuja

Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444

August 12, 2022
Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan

Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan

August 12, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.