Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta umarci Kwamishinan harkokin makamashi da albarkatun man Fetur, Hon. Sanusi Danfulani, da ya bayyana a gabanta ranar Talata, 5 ga watan Agusta, saboda gazawarsa wajen halartar ziyarar duba aiki da kwamitin majalisar mai kula da kimiyya da fasaha ya gudanar.
Ziyarar da aka shirya a ranar Alhamis ta sami tsaiko sakamakon rashin halartar Danfulani da wasu manyan jami’an ma’aikatarsa, lamarin da shugaban kwamitin, Awaisu Aliyu, ya bayyana a matsayin “wulakanci da sakaci da aiki da ga rashin mutunta majalisar dokoki.”
- Ma’aikatar Cinikayya Ta Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Soke Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Sin
- Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar
Aliyu ya ce, “An aika musu da sanarwa cikin lokaci game da ziyarar, amma babu wani jami’i daga ma’aikatar da ya halarta, sannan babu wani bayani na rashin zuwa daga gare su.”
Ya ƙara da cewa irin wannan sakaci yana tauye ikon da kundin tsarin mulki ya bai wa majalisar wajen gudanar da aikinta na sa ido. Don haka, ya umurci Danfulani da ya halarci zaman majalisar a ranar 5 ga Agusta ko kuma ya fuskanci hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp