Majalisar wakilai ta gabatar da ƙudirin kafa wata jiha mai suna Jihar Etiti a kudu maso gabas. Ƙudirin dokar ya samu goyon bayan ɗan majalisa Amobi Godwin Ogah da wasu mutane huɗu, inda aka yi karatu na farko yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Waɗanda suka ɗauki nauyin ƙudirin sun haɗa da ƴar majalisar wakilai Gimbiya Miriam Odinaka Onuoha (Okigwe/Onuimo), da ɗan majalisar wakilai Kama Nkemkama, da ƴar majalisar wakilai Gimbiya Chinwe Nnabuife, da kuma ɗan majalisa Anayo Onwuegbu.
- Barazanar Da Rashin Katabus Na Kananan Hukumomi Ke Yi Ga Dimokuradiyyar Nijeriya
- Sauya Fasalin Dimokuradiyyar Afirka: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Yada Kwallon Mangwaro Mu Huta Da Kuda
Ƙudirin dai na da nufin gyara sassa uku na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 domin maye gurbin lamba 36 da 37 domin karɓar sabuwar jihar da kuma ƙara jihar Etiti cikin jerin jihohin da ke cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Sabuwar Jihar Etiti da ake shirin kafawa za ta fito ne daga sassan jihohin Abia, da Anambra, da Ebonyi, da Enugu, da kuma Jihar Imo a yanzu, kuma za ta ƙunshi ƙananan hukumomi 11 da Shalƙwata a Lokpanta.
Kudirin ya kuma nemi a sauya jerin sunayen ƙananan hukumomi bisa ga jihohi da kuma mika ƙananan hukumomi 11 zuwa sabuwar jiha. Kananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Isuikwuato da Umu-Nneochi (Abia), Orumba North da Orumba South (Anambra), Ivo da Ohaozara (Ebonyi), Aninri, Agwu, da Kogin Oji (Enugu), da Okigwe da Onuimo (Imo).