A jiya ne majalisar dattawa ta zartar da kudirin kafa hukumar kula da yaki da yaduwar kananan makamai a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Majalisar ta amince da kudurin ne, biyo bayan nazarin rahoton kwamitin tsaro da leken asirin kasar.
- Babu Mafita Yanzu Game Da Karancin Man Jiragen Sama – Hadi Sirika
- An Gano Wani Gurbataccen Taki Da Ake Sayar Wa Manoma A Kano
Kudirin dai ya kunshi wasu kudirori uku – ragowar kudirorin biyu masu zaman kansu daya kuma daga bangaren zartarwa na gwamnati na adawa da yawaitar kananan makamai a kasar.
Bayan kammala karatun kudurin a majalisar dattawa, duk an mika su ga kwamitin tsaro da leken asiri na kasa don ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa.
Shugaban kwamitin Sanata Ibrahim Gobir (APC – Sokoto ta Gabas) a jawabin da ya gabatar a zauren majalisar, ya ce wadannan kudirori uku na neman samar da kafa wata hukuma ta gwamnati da za ta dora a kan yaki da yaduwar kananan makamai a Nijeriya.
A cewarsa kudurin ya bi sharin sashe na 24 na dokar ECOWAS ga wanda yake son mallakar makami.
Gobir ya ce kirkirar hukumar zai taimaka wajen rage yaduwar makamai a tsakanin al’umma duba da halin da kasar ke ciki na rashin tsaro.