Wata makala da mujallar Muhallin Halittu ta Nature ta Birtaniya ta wallafa, mai taken “Fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama na 2024 AI” da aka fitar a baya bayan nan, ta ce daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023, bisa mazanin “Nature Index”, kashi 6 cikin 10 na cibiyoyi masu binciken fasahohin AI da suka fi samun karuwar sakamako sun fito ne daga kasar Sin.
Mizanin “Nature Index 2024 AI”, ya nuna saurin karuwar fannin AI a cikin shekarun baya bayan nan da ba a taba ganin irinsa ba, da kuma mutanen da suka ba da yawancin gudummawa ga nazarin AI. Kididdigar ta nuna cewa, binciken AI da aka wallafa a Nature Index ya karu cikin sauri.
- An Gudanar Da Bikin Da Ya Shafi Makamashi Na Nan Gaba A Birnin New York
- Zaben Kananan Hukumomi: APC Ta Lashe Dukkan Kujerun Shugabanni A Kwara
Daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023, rabon binciken AI na Amurka ya kusan ninkawa sau biyu, yayin da kason hakan na kasar Sin ya karu da fiye da ninki biyar a tsakanin wa’adin. Kaza lika, ya zuwa shekarar 2023, Amurka ta hau matsayi na farko a fannin binciken AI, yayin da sauran kasashe biyar da ke kan gaba a fannin suka hada da Sin, da Jamus, da Birtaniya, da Faransa, kuma tazarar dake tsakanin Sin da Amurka ke kara raguwa cikin sauri.
Daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023, akwai cibiyoyi guda 10 dake samun karuwar binciken AI mafi yawa a mizanin “Nature Index”, wadannan suka hada da cibiyoyin bincike na kasar Sin guda 6, da suka kunshi cibiyar kimiyya ta kasar Sin, da jami’ar Peking, da jami’ar Tsinghua, da jami’ar Zhejiang, da jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Sin, da jami’ar Shanghai Jiao Tong. (Safiyah Ma)