Alkaluma daga hukumar lura da makamashi ta Sin ko NEA, sun nuna yadda makamashin da ake samarwa daga karfin iska da hasken rana ke taka muhimmiyar rawa, wajen samar da isasshen makamashi a kasar, kuma hakan ya biyo bayan fadada sassan 2 da aka jima ana yi.
A shekarar 2022, sabbin cibiyoyin samar da lantarki ta karfin iska da hasken rana da aka gina, sun samar da makamashin da ya kai kilowatt miliyan 120, yayin da jimillar makamashin da gaba dayan cibiyoyin samar da lantarki ta karfin iska da hasken rana suka samar a kasar ya zuwa karshen shekarar bara, ya zarta kilowatt miliyan 700.
Alkaluma sun nuna yadda sabbin cibiyoyin lantarki ta karfin iska da hasken rana da aka gina, ke samar da kaso 78 bisa dari, na jimillar sabbin cibiyoyin lantarki da Sin ta samar a bara, wanda hakan ya sanya su zama manyan ginshikai a fannin samar da lantarki. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp