Shugaban Makarantar Kogi State Polytechnic da ke Lokoja, Farfesa Salisu Ogbo Usman, ya bankaɗo wani gungun mutane da ke ƙirƙirar takardun kammala karatu na jabu a cikin makarantar. Wannan bincike ya kai ga dakatar da ma’aikata biyar, ciki har da magatakardar makarantar.
Farfesa Ogbo ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a Lokoja, da yammacin Laraba. Ya ce wannan harƙalla babban barazana ne ga mutunci da ƙimar makarantar.
- JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi
- Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga
A cewarsa, binciken da sashin ɗaukar ɗalibai da na bayanan zamani (ICT) suka gudanar, ya gano cewa wasu ɗalibai da ma’aikata ne ke haɗa baki wajen buga sakamakon bogi na difloma da babbar difloma don amfanin kansu. Ya ce tuni an dakatar da ma’aikatan da ake zargi yayin da ake ci gaba da neman wani mai suna Dominic Egwuda, wanda ake zargin yana cikin masu shirya wannan mummunan aiki.

Shugaban makarantar ya jaddada cewa ba zai yi sassauci ba ga duk wanda aka samu da hannu a irin wannan laifi. Ya kuma tabbatar da cewa makarantar za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren tabbatar da inganci da gaskiya, tare da dawo da amincewar jama’a da kare martabarta.















