Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da cewa dukkanin makarantun firamare da sakandare, na gwamnati da masu zaman kansu, za su fara hutun ƙarshen zangon karatu na uku a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025.
Wannan sanarwar ta fito ne daga Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru.
- Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
- Har Yanzu Yaƙi Da Ta’addanci Ne Babban Muradin Gwamnatina — Tinubu
A cewar sanarwar, dukkanin makarantun kwana da na jeka ka dawo za su tafi hutun.
An buƙaci iyaye da ke da yara s makarantun kwana da su zo su ɗauki ‘ya’yansu da wuri a ranar da aka fara hutun.
An kuma umarci ɗaliban makarantun kwana da su dawo makaranta a ranar Lahadi, 7 ga watan Satumba, 2025, yayin da ɗaliban da ke zuwa daga gida za su koma a ranar Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025.
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci.
Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp