Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya kada kuri’arsa a mazabarsa ta Gawuna a lokacin da ake gudanar da zabukan gwamnola da na ‘yan majalisar jiha, inda ya ce makomarsa tana hannun Allah.
Gawuna ya ce yana da yakinin cewa za a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali kamar yadda aka samu cikakken tsaro.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wakilan PDP 2 Suna Sayen Kuri’a A Ogun
- Ya Kamata Jami’an Tsaro Su Sake Dagewa —Abba Gida-Gida
“Iko daga Allah yake kamar yadda nake fada, kuma ko kadan ban damu ba domin nasan Allah ya riga ya kaddara wanda zai lashe wannan takara,” in ji shi.
Gawuna ya bayyana cewa, fitowar masu kada kuri’a ma abin yabawa ne domin tun karfe 8 na safe kusan daukacin rumfunan zabe a Kano sun yi wa masu kada kuri’a kawanya.
Haka zalika, dan takarar na APC ya yabawa INEC kan shirye-shiryen da take yi da kuma saurin jigilar kayayyakin zabe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp