Sama da ma’aikatan ilimi 1,700 na makarantu 110 a fadin kasar nan ne, suka koka kan gazawar gwamnatin tarayya na gaza biyan bashin albashin shekaru uku da suke bi.
Malaman da suka fusata a wata budaddiyar wasika da suka aike wa sakatare kuma ministan ilimi, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan su bashin albashinsu na shekaru uku.
- Bam Ya Yi Ajalin Mutane 20, Ya Jikkata 2 A Yobe
- Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Zai Dade Bai Farfado Ba – AFDB
Sun ce an dauki malaman aiki a 2018, 2019 da 2020, kuma ba a biya su albashi ba tun lokacin da aka dauke su aiki.
A cewarsu an dangantaka rashin biyan albashin da matsaloli iri-iri ciki har da tsarin biyan albashi na IPPIs.
“A cikin shirinmu na gama-gari, muna neman a biya mu kudaden da muka dade muna bi.” A matsayinmu na malamai, ba mu manta da matsayinmu na masu baj wa al’umma tarbiyya ba. Duk da haka, ba za mu iya tsara makomar al’ummarmu tare da damuwa ba ta hanyar yunwa da bashi,” in ji su.
“Muna kira da a tausaya mana a ji kanmu saboda matsin rayuwa da ake ciki,” in ji su.