A daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke gargaɗin ‘yan Nijeriya kan samun mamakon ruwa, wanda ka iya haddasa ambaliyar ruwa a wasu daga cikin jihohin wannan ƙasa, sai ga shi kwatsam, mamakon ruwan saman na barazanar hana mutane harkokin yau da yau da kullum a wasu jihohin.
Mamakon ruwan sama, ya yi wa al’umma Jihar Filato ɓarna, a daidai lokacin da kuma ambaliyar ruwa ta mamaye gonaki a Jihar Neja tare da katse hanyar yankin kogi ta Gabas da ke faɗin jihar. Lamarin ya faru ne a yankin Arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Har ila yau, wata guguwar iska, ta lalata gidaje kusan aƙalla 50 a unguwar Menkaat (gundumar Shimankar) da ke Ƙaramar Hukumar Shendam ta Jihar Filato.
- Mamakon Ruwan Sama A Wasu Jihohi Na Barazana Ga Harkokin Yau Da Kullum
- Remi Tinubu Ta Bada Gudunmawar Naira Biliyan 1 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwan Neja Ta Shafa
Bincike ya nuna cewa, wata guguwa da ta biyo bayan ruwan sama, ta yi matuƙar ɓarna ƙwarai da gaske, tun a ranar safiyar Lahadi.
Kazalika, ɓarnar ta fi shafar makarantu da kuma wuraren ibada da ke yankin na ƙaramar hukumar.
Mazauna yankin, sun shaida wa wakilinmu cewa; kimanin gidaje hamsin (50) ne rufin gidajen nasu ya kwaye, yayin da kuma wasu gine-gine nan take suka rushe.
Wani mazaunin yankin da abin ya shafa, Mista Lawrence Longwalk, ya koka da yadda lamarin ya afku tare kuma da yin kira ga hukumomin da abin ya shafa, da su gaggauta shiga cikin lamarin, domin kawo ɗaukin gaggawa.
“Guguwar ruwan saman, ta yi matuƙar yi wa mutanenmu ɓarna. Lamarin da ya faru da sanyin safiyar Lahadi.”
Har ila yau, ya ƙara da cewa; guguwar ruwan saman, ta kuma lalata wasu wuraren ibadu da kuma makarantu da dama a yankin namu.
A cikin kalaman nasa ya nuni da cewa, “Ganin yadda ɓarnar ta munana, mutane na buƙatar agajin gaggawa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Guguwar ruwan saman, ta mamaye wasu makarantun firamare guda biyu da wuraren bauta da ke wannan gunduma ta Shimankar baki-ɗaya.
Sai dai, yayin da wasu ƙarin filayen noma da ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da su a ƙarshen makon da ya gabata a jihar ta Neja, gwamnatin jihar ta umarci waɗanda suke zaune a wurin da iftila’in ya afku, su gaggauta tattara kayansu su bar wajen.
LEADERSHIP ta tattaro bayanan cewa, al’ummar da ke Kafin Koro ta Ƙaramar Hukumar Paikoro da kuma wasu garuruwa 18 da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta jihar, ambaliyar ta yi awon gaba da su.
Garuruwan su ne; Dere, Eshi, Apataku, Tsakanabi, Kuchi Kakanda, Arah, Achiba, Rebba, Ebwa, Pele, Edda, Rigido, Gbami, Yawa, Baka da kuma Muye.
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Hon. Jonathan Ɓatsa, ya tabbatar da afkuwar wannan al’amari, inda gonaki da dama ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da su, sannan kuma ya buƙaci mazauna wuraren da ke jihar da su gaggauta barin wuraren, sakamakon yadda ruwan saman ya tsananta a dukkanin faɗin jihar a halin yanzu.
Ya kuma yi kira ga al’ummar yankunan da abin ya shafa, da su gaggauta komawa wuraren da ba su da matsala, domin kaucewa wannan annoba da ta kunno kai jihar.
Ɓatsa ya ƙara da cewa, “Duk da cewa, gwamnati ta fahimci waɗannan mutane suna zaune ne a gidajen da suka gada kaka da kakanni, amma kuma ya kamata su yi biyayya ga gargaɗin gwamnatin na barin wuraren da suke zaunen, har sai bayan damina ta shuɗe.”
“Mu a matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da himma wajen yin kira ga jama’a, musamman waɗanda ke yankunan da ambaliyar ruwan ta mamaye, da su gaggauta tashi su koma wasu wuraren daban, don gudun ka da su tsinci kansu a irin iftila’in da ya faru a Mokwa.
“Ba za mu taɓa mantawa da tashin hankalin da muka shiga sakamakon iftila’in da ya afku a Mokwa ba, har yanzu muna jin raɗaɗin abin, sannan kuma ba za mu sake barin hakan ta sake faruwa ba, shi yasa gwamnati ke ci gaba da kiraye-kiraye ga jama’a da su gaggauta matsawa zuwa wasu wuraren daban, don gudun ka da al’amarin ya rutsa da su,” kamar yadda ya bayyana.
Ƙaramar Hukumar Idah da ke yankin Kogi ta gabas, ta yanke gaba-ɗaya daga Lokoja, babban birnin jihar; sakamakon wannan ambaliya ta ruwa da ta yi sanadiyyar rugujewar wasu manyan gadoji da ke haɗe da juna.
Idan ba a manta ba, Idah na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi tara da ambaliyar ruwan ta shafa a jihar. Sauran ƙananan hukumomin sun haɗa da Ibaji, Ofu, Kogi, Ajaokuta, Bassa, Lokoja, Adaɓi da kuma Igalamela.
Wani ganau ba jiyau ba, mai suna Alhaji Ali Atabor, shi ne ya bayyana wa Leadership hakan, a cikin saƙon nasa ya ce, “Abin da ke faruwa a hanyar daga Ajegwu zuwa Okpachala zuwa Idah a halin yanzu, a cikin awa ɗaya da ya wuce hanyar a tsaye take cak, babu zirga-zirga kwata-kwata,” in ji shi.
Wannan dalili ne ya sa, al’umma suke kira ga hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jhiar Neja da su yi wa Allah su kawo musu agajin gaggawa.
Wani ɗan yankin Ƙaramar Hukumar Idah, Salisu Isah, ya shaida wa wakilinmu cewa; hanya ɗaya ce tak ta shiga Lokoja, yanzu sai dai a bi ta hanyar Anyigba, mai nisan kilo mita da dama daga Idah. Wannan shi ne halin da ake ciki a wannan babbar hanya ta daga Ajegwu zuwa Opkachala zuwa kuma Idah.
Duk da wannan ɓarna ta ambaliyar ruwa da ake samu a wasu jihohi, wasu jihohin kuma kokawa suke yi kan matsalar ƙarancin samun ruwan saman. Jihohi kamar irin su; Jigawa, Katsina, Sakkwato, Kano da sauransu; na fama da ƙarancin samun ruwan saman a wasu ɓangarorin.
Kamar yadda wakilanmu suka shaida mana, wasu ɓangarori da dama na waɗannan jihohi, har sai da ta kai ga an fara addu’o’in roƙon samun ruwa. Rahotanni sun tabbatar da cewa, a Jihar Kano; ruwan saman ya fi samuwa ne a cikin ƙwaryar birni, fiye da sauran yankunan karkara.
Haka nan, a Jihar Jigawa ma suke fama da wannan matsala ta ƙarancin samun ruwa, wasu ɓangarorin akwai ruwan; wasu kuma ruwan ya yi ƙaranci.
Kazalika, Jihar Kaduna ma haka matsalar take; kamar yadda rahotanni suka bayyana, wasu ɓangarorin na samun mamakon ruwan saman, wasu kuma ruwan ya yi ƙaranci ƙwarai da gaske.
Jihohi da dama na faɗin wannan ƙasa, sun samar da taki ga manoma a farashi mai sauƙi, sai dai kuma sai ga shi wasu daga cikin jihohin na fama da matsalar ambaliyar ruwa, wasu kuma na fama da matsalar samun ƙarancin ruwan saman baki-ɗaya.
Babu shakka, wannan ba a abu ne mai daɗi ba; musamman ganin yadda a daidai wannan lokaci, gwamnatin tarayya ke ci gaba da ƙoƙari, wajen aiwatar da shirinta na wadata ƙasa da abinci a dukkanin faɗin ƙasar.
Har ila yau, kowa shaida ne ganin yadda farashin abincin yake ci gaba da faɗuwa warwas a kasuwannin sayar da abinci, kama daga kan Masara, Wake, Shinkafa, Gero, Dawa, Waken suya da sauran makamantansu.
Gwamnati, na aiwatar da wannan shiri ne, don ƙoƙarin ganin kayan abinci da sauran kayan masarufi sun sauƙi, musamman ga talakan da ba shi da cin yau, ballantana na gobe.
Koda-yake, a wani ɓangaren kuma, ƙungiyoyin manoma da dama na faɗin ƙasar nan na ci gaba da yin Allah-wadai da wannan sabon shiri na gwamnatin tarayya, domin a cewarsu; an ɗauki wata hanya ne karya su ko kuma ma hana yin noman baki-ɗaya.
Ƙungiyoyin, sun zargi gwamnatin tarayyar da ɗaukar hanyar da ba za ta ɓulle ba, maimakon bayar da tallafi ga Takin zamani da sauran kayan ayyukan noma, waɗanda za su taimaka musu wajen ayyukan nasu na noma a cikin gida, sai gwamnatin ta ɓuge da shigo da waɗannan kayayyakin abinci daga ƙasashen ƙetare.
Bugu da ƙari, yadda alamu suke nunawa; babu shakka a bana, kayan abinci za su samu tare kuma da matuƙar yin sauƙi, amma a gefe guda kuma; akwai yiwuwar manoma da dama za su shiga halin ha’ula’i, ta hanyar tafka mummunar asara, sakamakon ambaliyar ruwa, ƙarancin samun ruwan sama a wasu jihohi da kuma wannan shiri na gwamnatin tarayya na shigo da kayan abinci daga ƙasashen ƙetare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp