Mai shiga tsakanin masu garkuwa da wadanda aka yi garkuwa da su don biyan kudin fansa, Tukur Mamu, wanda ake tuhumarsa da aikata laifukan ta’addanci, ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja, da ta dauke shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) zuwa gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja.
Mamu ya roki mai shari’a Inyang Edem Ekwo da ya sauya hukuncin da aka yi masa na ci gaba da zama a hannun DSS.
- Hukumar NCAA Ta Karyata Rahoton Sayen Mota Ta Fiye Da Naira Miliyan 250
- JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike
A yayin zaman shari’ar a jiya Litinin, Mamu ta bakin lauyansa, Abdul Mohammed (SAN), ya shaida wa kotun cewa, umurnin da ta bayar na ranar 19 ga watan Disamba, 2023, na cewa a bar likitansa ya duba shi domin kula da lafiyarsa, DSS ba ta mutunta wannan umurnin ba.
Mamu ya yi zargin cewa, ba a ba wa likitansa damar ganinsa ba, kuma yana bukatar kulawa ta gaggawa a kowane asibiti a fadin Nijeriya.
Ya kara da cewa, zai iya rasa ransa a kowane lokaci idan ba a dauke shi daga hannun DSS zuwa gidan yarin Kuje ba.