Kafafen yada labarai da dama sun kawo rahoton cewa Shuban kasa Muhammadu Buhari ya kafa tarihi na soma hako mai a yankin Arewa, amma abun tambayar shi ne ya ya wannan aikin zai kasance?
A yanzu dai za a iya murnar hakan, mafi yawan mutane sun kosa su ga an soma samar da wannan man a Arewacin Nijeriya da gaske. Abun dubawa shi ne Shugaba Buhari bai sanya lokacin da za a fara gudanar da harkokin kasuwanci a Kolmani ba; ma’ana a sami man da gaske. Rashin tsara lokacin ya sanya tababa a zuciyar mutane wanda ake iya tuna tarihi na wasu manyan ayyuka da aka tsara a Nijeriya.
Ba wai ina tababa na yarda da rubutun ra’ayin Edita na Jaridar Daily Trust ba ne da ya yi masa kanu da cewa; ‘Muna murna da samun man Kolmani a Arewacin Nijeriya’, amma na sanya alamar tambaya.
Akwai shawarwari guda uku ga gwamnati da za su kara tabbatar da nasarar wannan tarihin ci gaba na gwamnatin Buhari.
Na farko, roko ne ga gwamnatin Buhari ta tabbatar da dokar wannan aiki na mai a Kolmani ya zamana cewa an sanya shi a bisa doka da tsari kafin Buhari ya bar mulki.
Haka kuma, fahimta na nuna mun cewa Buhari zai ga wannan shawarar kamar wani abu ne mai wahalar gaske.
Ba na son in zama mai saurin karaya, amma ire-iren wadannan shawarwari ba sa yi wa wannan gwamnati amfani. A wajensu kaddamar da samar da mai na Kolmani ya isar masu, kuma jama’a sun yi masu godiya wanda shi ne bukatarsu.
Kasa da makonni 25 suka rage wa gwamnatin Buhari, kuma ya kamata ya yi wani abu da ba za a manta da shi ba. An bar ayyukan da ba a kammala ba, kamar aikin hanyar Abuja zuwa Kano da ake yi yanzu haka, da aikin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna na Jonathan ko kuma aikin yashe kogin Neja na ‘Yar’Adua, ya kuma tabbatar da cewa aikin Kolmani na samar da mai da ya fara an fara samar da man fetur da gas a wurin a cikin watanni 6 masu zuwa.
Kafin a fitar da rai, ya kamata a yi murnar samun nasarar wannan aikin. A maganganun irin na siyasa nasarar samun wannan man zai kawar da gori da ake yi wa yankin Arewa na cewa suna dogaro da mai da ake samowa a yankin Kudancin Nijeriya. Yanzu wani ce-ce-ku-ce kan albarkatun kasa bai zama abun tattaunawa ba.
A bangaren tattalin arziki kuwa, yankin dai yana cikin kangin talauci. Akwai mutum miliyan 20 da suke fama da kuncin talauci a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Samun jiha daya ko biyu a yankin sun shiga cikin jihohin da suke samar da man fetur a Nijeriya za a ga kudaden da yankin ke samu ya karu ala-akalla. Za a sami masu zuba jari a yankin da ayyukan yi da kuma karin samun walwala da jin dadin mutanen yanki. A takaice ma dai, mutanen Gombe da Bauchi ba za a rika zolayarsu da cewa kudaden talakawa ne suke yin bulbul ba.
Kuma wani abu da ya kamata mu duba sosai a kai shi ne, dole mu kula da lalacewar muhallin jihohin da kuma sauran makwabtan jihohi.
Babban abu mai kyau da gwamnati za ta iya yi, ta dauki darasi ga malalar mai a yankin Neja Delta da yadda kamfanoni suka kasa daukan mataki a kan lamarin. Ba kamar yankin kudu ba, malalar mai a Bauchi yana da matukar matsala ga ruwan sha a Nijeriya wanda ya hade da kogin Benuwai.
Harkokin noma da wurin shakatawa da suke wurin kamar Yankari za su iya samun matsala.
Za mu iya fatan cewa gwamnati ta dauki darasi daga yadda mutane suke zato kamar yadda aka yi da yashe kogin Neja. Muna fatan aikin samar da man Kolmani kar a yi wasti da shi da nuna halin ko-in-kula kamar yadda aka yi da kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta.
Dole Buhari ya tabbatar da an yi abun da ya dace wajen yiwuwar abun. Idan ba haka kuwa, babu wanda zai rika tunawa da kokarinsa. A gaba daya Nijeriya tana hako man fetur tun tsawon shekara 66, amma mutane da yawa ba sa iya tuna tsohon shugaban kasar da ya assa samar da hako man.
Abun da nake tunani shi ne, zan so in ga yadda aka kaddamar da wannan wurin samar da mai na Kolmani, an hako man an kai wurin tace man inda za mu iya ganin man a zahiri. Amma saboda rashin matatun mai da suke aiki a kasa, za mu rika ganin jiragen ruwa dauke da danye mai ana fita da su kasashen waje kamar yadda ake yi a yanzu.
Lallai wannan yana bukatar lokaci a gina hanyar bututun mai da wuraren ajiye man da hanyoyi da tankunan mai da makamantansu. A wannan fa makonni 25 kacal suka rage wa wannan gwamnatin kuma abu ne mai wuya a iya hakan.
Wani abun tantama a kan wannan shi ne, a lokacin da Shugaban NNPC, Mele Kyari ya bayar da sanarwar cewa sun kammala komai har da bayar da kudi don gina matatar mai. Al’umma dai sun san cewa kamfanin NNPC bai ajiye ko sisin kobo ba a asususn ajiyar gwamnatin tarayya a gaba dayan shekarar nan, wannan magana ya zubar wa da Kyari mutunci a idon ‘yan Nijeriya. Idan muka kara da wannan na gazawarsa zuwa da gano barayin mai da tallafin mai da ake biya, za mu tsinke da lamarin.
A batun gaskiya, gina matatar mai yakan kai shekara 4 zuwa 6 a tsarin Nijeriya. Babban misali shi ne matatar mai ta Dangote, wanda da yardar Allah an kusa fara amfani da ita. Mutane da dama suna fatan rijiyar mai na Kolmani zai fara aikin kwanan nan.
Mutane masu kallon al’amuran yau da kullum cikinsu kuwa har da ni, muna fatan mu ji tsarin kasa da watannin 12. Kamar sanya bututun mai zuwa Kaduna aikin da yake da wahalar gaske ga kuma tsada. Amma ba a nan gizon ke saka ba. A saboda haka yake da matukar wahala ka nuna wa mutane cewa wannan abu da aka yi ba an yi ne don yaudarar masu zabe a 2023.
Don kara jaddadawa, kamar yadda kowani dan Arewa da ke kishin yankin yake, ina matukar murna da jin dadin samun man fetur a yankin. Samun kammalallen aikin zai warware matsaloli daban-daban da fasa kwabrin mai da ake kaiwa kasashe makwabta musamman idan kamfanoni masu zaman kansu suka shiga harkar. Nasarar samun mai a wannan yankin zai kara ingancin kungiyar ECOWAS.
Yankin zai amfana sosai tun daga tsaro da samar da daidaitaccen tattalin arziki wanda zai kawo karshen ta’addanci. Fara hako mai zai sauya siyasar Nijeriya ta yadda Arewa za ta kara samun wata dama baya ga yawan da take da shi na jama’a. Lallai wannan shi ne abun da ake fata wanda ba za a samu ba har sai an fara hako wannan mai kuma ana amfani da shi.
A saboda haka, idan Buhari yana son wannan abu na samar da mai ya yiwu ba wai a takarda ba, dole ya samar da abubuwan da suka kamata na doka a kai don ganin ana hako mai a Kolmani. Idan ba haka ba kuwa tarihi zai rika tunawa da gwamnatin da ta kammala aikin ne ba wacce ta fara aikin ba.