Manchester United ta tabbatar da daukar Ruben Amorim a matsayin kocin babbar tawagar kungiyar.
Amorim zai koma Manchester domin ci gaba da aiki inda kwantiraginsa zai kare a watan Yunin shekarar 2027 tare da zabin karin shekara guda idan ya taka rawar gani.
- Senegal Ta Kulla Yarjejeniyar Gudanar Da Aikin Karkatar Da Ruwa Da Kamfanin Kasar Sin
- Matsalar Almajirai Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta Kalubale Ga Shugabannin Arewa – Sultan
Zai kama aiki a ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba kamar yadda yake a sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Juma’a.
Idan za a tuna LEADERSHIP Hausa, ta ruwaito cewa kungiyar ta kori Eric Ten Hag bayan ya shafe shekaru biyu da rabi yana aiki a matsayin kocin kungiyar.
Wannan na zuwa ne bayan wani hukunci da kungiyar ta yanke jim kadan bayan rashin nasara da suka yi da West Ham da ci 2-1 a ranar Lahadi.
Manchester United na fatan ganin ta dawo cikin ganiyarta da kuma ci gaba da lashe kofuna musamman kofin gasar Firimiya wanda tun bayan barin Sir Alex Ferguson kungiyar ba ta sake dauka ba.