Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta samu nasara bayan doke Athletico Bilbao a wasa na biyu da suka kara a filin Old Trafford, lamarin da ya kai ta wasan ƙarshe na gasar Europa.
Man Utd ta doke Bilbao da ci 3-0 a wasan farko, sannan ta ƙara samun nasara a wasan na biyu da ci 4-1.
- Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali
- Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?
Wannan ne ya tabbatar da cewar ƙungiyar ta kai wasan ƙarshe na gasar a karon farko cikin shekaru takwas.
Ko da yake tana matsayi na 15 a teburin gasar Firimiyar Ingila, wannan nasara ta nuna cewa har yanzu ƙungiyar na da damar lashe kofi a bana.
Kocin ƙungiyar, Ruben Amorim, ya danganta wannan nasara da goyon bayan magoya bayan ƙungiyar.
A ranar 21 ga watan Mayu, Manchester United za ta kara da Tottenham Hotspur a wasan ƙarshe da za a buga a filin wasa na San Mames da ke birnin Bilbao, a ƙasar Sifaniya. Tottenham kuwa na fatan lashe kofin Turai na farko.
Za a jira a gani wacce ƙungiya ce za ta ɗauki kofin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp