Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta zama zakarar gasar zakarun turai ta 2023 bayan doke Inter Milan da ci daya mai ban haushi.
An fara wasan ne da misalin karfe 8 agogon Nijeriya, a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Dan wasan tsakiyar Manchester City, Rodri ne ya zura kwallo guda daya tal, da ta raba gardama a wasan.
Tun da fari dai an yi hasashen Manchester City na iya lashe gasar.
Manchester City ta samu gurbin zuwa wasan karshe na gasar bayan doke Real Madrid da ci 4 da babu a filin wasa na Etihad da ke Ingila.
Mai horar da Manchester City, Pep Guardiola ya sake lashe kofin a karo na biyu da kungiyoyi daban-daban.
Ya taba lashe kofin da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.