Manchester United na da ƙwarin gwuiwar amincewar sabon kwantiragi da kyaftin Bruno Fernandes a cikin ‘yan makwanni masu zuwa.
Kwantiragin ɗan wasan wanda ya ƙulla a shekarar 2022, zai ƙare a shekarar 2026, mai yiyuwa ne a bayar da sanarwar kafin rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a ranar 30 ga watan Agusta, amma babban abin da shugabannin United ke mayar da hankali a kai a halin yanzu shi ne ƙulla yarjejeniyar da za ta ƙara wa’adin zaman sa a Old Trafford.
- Liverpool Ta Bayyana Arne Slot A Matsayin Wanda Zai Maye Gurbin Klopp
- Manchester City Na Buƙatar Yuro Miliyan 77 Kafin A Ɗauki Ɗan Wasan Gabanta
Fernandes ya maye gurbin Harry Maguire a matsayin kyaftin ɗin ƙungiyar a shekarar 2023 kuma Erik ten Hag ya ɗora imaninsa a kan ɗan wasan tsakiyar, duk da sukar da ya fuskanta a wasu lokuta daga tsoffin yan wasan United Gary Neville da Roy Keane.
Babu sunan Fernandes mai shekaru 29 a cikin yan wasan da United za ta saurari tayin wasu ƙungiyoyin da suke neman yan wasanta.
Ɗan wasan ya buga minti 90 a ranar Asabar, yayin da aka doke United a bugun fenariti bayan da suka tashi 1-1 a wasan ƙarshe na Community Shield da Manchester City.