Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi ban kwana da FA Cup na bana, bayan kungiyar Fulham ta doke ta da ci 2-1 a filin was ana Old Trafford ranar Lahadin da ta gabata.
Manchester United ce ke rike da kofin da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, kofin da ya ba ta damar buga Europa League a kakar nan.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [1]
- Adadin Mata Mamallaka Sana’o’i Na Ta Karuwa A Kasar Sin
Kungiyar da take buga wasa a filin wasa na Old Trafford tana ta 14 a kasan teburin Premier League da maki 33, bayan da ta ci wasa tara da canjaras shida aka doke ta fafatawa 12.
Rabon da kungiyar ta yi irin wannan rashin kokarin tun bayan shekarar 1974 da ta fadi daga babbar gasar ta Ingila. Kofin Premier League na karshe da United ta dauka tun shekarar 2012 zuwa 2013, lokacin da Manchester City ta yi ta biyu da tazarar maki 11, kuma na 20 da United ta lashe. Daga nan Manchester City ta karbe ragamar lashe babban kofin na Ingila, Chelsea ta dauka sau biyu da Leicester City mai daya,
Liverpool ta dauka a 2020.
Liberpool na shirin lashe Premier League na bana kuma na 20 jimilla, za ta yi kan-kan-kan da yawan wanda Manchester United ta dauka a tarihi kuma Liberpool ce ta daya a kan teburin Premier na kakar nan da maki 67, sai Arsenal ta biyu mai maki 54.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp