Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kammala daukar dan wasan tsamiyar Real Madrid, Carlos Henrique Casemiro.
Casemiro zai rattaba wa Man United hannun shekara hudu.
- Yanzu-Yanzu: Kwamishinan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Nasarawa Ya Kubuta
- Za A Rataye Dan Damben Da Ya Kashe Matarsa
Kungiyar ta biya fam miliyan 60 da karin fam miliyan 10 ga Real Madrid.
Dan wasan zai kasance daya daga cikin wanda suka fi kowa daukar kudi a Manchester United.
Casemiro ya shafe shekara tara da Real Madrid, inda ya lashe kofi 18, sannan ya zura kwallo 31 a raga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp