A makon da ya gabata Manchester United ta buga canjaras a wasan da Real Sociedad na gasar Europa League zagaye na farko a filin wasa na Reale Arena dake Sen Sebastian.
Amma Man Utd ɗin ta gasgata abinda bahaushe ke cewa kowa a gidansa Sarki ne bayan ta zazzagawa Sociedad ƙwallaye 4 a raga, da kuma wannan sakamakon ne United wadda Ruben Amorim ke jagoranta ta tsallaka zuwa matakin na kusa da na kusa da na karshe a gasar ta Europa League.
- Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028
- Bayan Shekaru 115 Manchester United Za Ta Gina Sabon Filin Wasa
Kyaftin din masu masaukin baƙin Bruno Fernandes ne ya zura ƙwallaye uku rigis a wasan kafin Diogo Dalot ya jefa ta huɗu, duk da cewar United ɗin aka fara jefa wa ƙwallo a raga amma hakan bai sa sun yi sanyin gwuiwa a Old Trafford ba.
Yanzu Manchester United za ta hadu da Olympic Lyon ta ƙasar Faransa a wasan zagayen na kusa da na ƙarshe da za a buga ranar 10 ga watan Afrilu mai kamawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp