Leny Yoro ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 5 a matsayin sabon dan wasan Manchester United.
Leny Yoro ya rattaba hannu kan kwantiragi a Man United yayin da kulob din da ke buga gasar Premier ya sanar da siyan Yoro akan Yuro miliyan 62.
- Gwamnatin Kaduna Ta Nisanta Kanta Akan Bidiyon Dukan Dan Balki Kwamanda
- Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Takardar Neman Kara N6.2trn A Kasafin Kudin Bana
Manchester United ta doke kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a cinikin tsohon dan wasan na Lille mai shekaru 18 domin komawa Old Trafford don cigaba da taka leda.
Dan wasan tsakiyar, zuciyarsa na son komawa Real Madrid amma zakarun na La Liga sun gagara biyan kudin da Lille ta nema na dan wasan saboda ya rage saura shekara daya a kwantiraginsa da kulob din na Ligue 1.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp