Wasu rahotanni daga Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta kai sabon tayin kudi fam miliyan 70 domin sayan dan wasan Barcelona, Frankie De Jong.
Manchester United dai ta dade tana zawarcin matashin dan wasan mai shekara 25 kuma tuni ya amince da komawa kungiyar duk da cewa ba zata buga wasannin cin kofin zakarun turai ban a Champions League na bana.
- Ganduje Ya Nada Baffa A Matsayin Shugaban Hukumar Kare Hakkin Masu Siye Da SiyarwaÂ
- Chelsea Tana Tattaunawa da Manchester City Kan Sayalen Sterling
Sabon kocin Manchester United, Erik ten Hag, ne yake fatan sake haduwa da dan wasan, wanda ya taba koyarwa a lokacin da suka yi aiki a Ajax ta kasar Holland.
A kwanakin baya dai Barcelona ta yi fatali da tayin kudi na fam miliyan 60 da Manchester United ta yi a kan dan wasan, sai dai ana fatan a wannan lokacin idan Manchester United ta sake kai sabon tayin kudin za a daidaita.