Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Sadio Mane, ya lashe kyautar Gwarzon dan wasan da babu kamarsa a Nahiyar Afirka.
Mane, wanda ya taimaka wa kasarsa ta Senegal, ta lashe kofin Nahiyar Afirka a farkon wannan shekarar, ya doke tsohon abokin wasansa a Liverpool, Mohamed Salah da mai tsaron ragar Chelsea, Edourdo Mendy, wanda shi ma dan Senegal ne.
- Halin Da Ake Ciki A ‘Yandoton Daji Bayan Nadin Sarautar Dan Ta’adda
- Zargin Almundahana: Yau EFCC Za Ta Gurfanar Da Tsohon Akanta-Janar A Gaban KotuÂ
Wannan dai shi ne karo na biyu da dan wasan mai shekara 30 yake lashe wannan kyautar bayan ya lashe a 2019.
Mane dai shi ne ya zura kwallon karshe a bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan karshe da suka doke kasar Masar a kofin da aka buga a kasar Kamaru.
“Na sadaukar da wannan kyautar ga matasan kasar Senegal, ban san me zance ba saboda farin ciki” a cewar Mane, bayan an ba shi kyautar.