Mahajjata hudu – daya daga Maroko sauran kuma daga Sifaniya – sun isa kasar Saudiyya a kan dawakai a wannan makon da ya fice don gudanar da aikin Hajjin 2025, wanda hakan ke tunatar da al’ummar Musulumi tsarin zuwa aikin hajji a shekaru da dama da suka gabata.
Mahajjatan sun isa zuwa kasar Saudiyya ne ta kan iyakar Al Hadithah da ke Al Qurayyat, inda jami’an gwamnati suka tarbe su tare da duba lafiyarsu, da kuma basu abubuwan sha don jinjin irin tafiyar da suka yi ta tsawon makonni.
- Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe
- Nijeriya Ta Yi Asarar Naira Biliyan 118 Sakamakon Barnatar Da Iskar Gas A Watanni 2
Hotunan yadda suka yi kura amma cikin nasara sun bazu a yanar gizo, inda suka nuna aniyarsu ta isa Makka ta hanyar amfani da hanyoyin tafiye-tafiye irin na tarihi.
“Wannan irin tafiya, tana nuna tsantsar ibada ga Ubangiji,” in ji Mamdouh Al Mutairi, shugaban ofishin kan iyakar Al Hadithah, wanda da kansa ya gaishe da mahayan.
Zabin mahayan na ratsa hamada da tsaunuka ya nuna yadda mahajjata ke tafiye-tafiyen aikin Hajji kafin fara amfani da ababen jigilar kayayyaki na zamani.
Jami’an Saudiyya sun dauki nauyin duk wata buƙatar mahayan ta musamman. Wannan tafiya ta haifar da muhawara a duk duniya game da daidaita al’ada da zamani a cikin ayyukan addini.
Kamar yadda sama da mahajjata miliyan 1.8 ke shirin Hajjin 2025, wannan yunkuri ya fito fili a matsayin shaida na dawwama da imani da juriya akan mabiya addinin Musulunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp