Wasu daga cikin manoman kasar nan, sun bukaci Shugaban Kasa; Bola Ahmed Tinubu, ya kara yawan adadin wadanda za su amfana a tallafin bunkasa aikin noma da gwamnatin tarayya ta kirkiro da shi a kasar.
Sun gabatar da wannna bukatar ce, a makon da ya gabata a martanin da suka yi bayan jawabin da Shugaba Tinubu ya yi wa masu gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwar da barke a wasu daga cikin sasaan wannan kasa, inda shugaban ya shelantan cewa; zai samar wa da manoman kasar kayan habaka aikin noma.
- Kudaden ‘Yan Majalisa: Wa Za A Gaskata Tsakanin Hukumar Albashi Da Kawu Sumaila?
- Gwamnatin Sakkwato Za Ta Siyo Shinkafar Biliyan 14 Don Sayarwa A Farashi Mai Sauki
A cewar manoman, alkawarin da shugaba Tinubu ya yi na habaka fannin noma a kasar, ko kadan bai isa ba; har sai idan ya sanya miliyoyin manoman kasar a cikin shirye-shiryen gwamnatinsa na bunkasa fannin.
Daya daga cikin manyan manoma a kasar kuma shugaban kungiyar dilolin sayar da kayan manoma na kasa (NAIDA), Kabir Umar Fara ya bayyana cewa, kamata ya yi gwamnatin ta yi abin da ya dara haka.
Kabir ya ci gaba da cewa, tallafin da gwamnatin za ta bayar; ba zai wani taka kara ba, domin ba zai isa ga manoma sama da 200’000 da ke daukacin jihohi 36 na kasar nan ba; ciki har da babban birnin tarayyar Abuja.
Haka zalika, shugaban ya yi kira ga Shugaba Tinubu; da ya jawo masu ruwa da tsaki da sauran kungiyoyin manoma, musamman domin su fahimci kalubalen da manoman kasar ke ci gaba da fuskanta, domin a samar musu da goyon bayan da ya kamata.
A cewarsa, a lokacin noman rani; kimanin manoman Alkama 200,000 ne aka taimaka wa da kuma karin wasu manoman ranin kimanin 100’000.
Ya kara da cewa, akwai kuma bukatar a taimaka wa kimanin kananan manoma 200,000, inda ya yi nuni da cewa; idan har ana so a samar da dauki a fannin aikin noman, manoman kasar za su iya samar da kashi 25 a cikin dari na amfanin gona a kasar, inda kuma gwamnatin za ta samar da rangwamen da ya kai kashi 75 cikin dari; wanda hakan zai kai har zuwa ga sauran manyan manoma.
Har ila yau, ya yi nuni da cewa; a halin yanzu buhun takin zamani daya na samfarin NPK kudinsa ya kai kimanin Naira 45,000, ya ake so kuma manomi ya iya sayen sa a kan wannan farashin?
Kabiru ya kara da cewa, da za a ci gaba da tsarin noma irin na tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, manoman kasar nan za su iya sayen kayan aikin noma a cikin farashi mai sauki.
Shi ma a nasa bangaren, shugaban kungiyar manoma na kasa (AFAN), Kabiru Ibrahim ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya ba ta da wadatattun kudaden da za su kai ga sauran kananan manoma, amma kamata ya yi ta samar da kyakkyawan yanayi ga manoman kasar, domin samun damar kara habaka fannin.
Shi kuwa shugaban kungiyar masu sarrafawa da sayar da takin gargajiya na kasa (OFPSAN) Noel Keyen, ya nuna damuwarsa a kan ayyana dokar ta-baci da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi, a fannin aikin noman kasar; amma ta gaza zuba wadatattun kudaden da suka kamata a cikin shirin na habaka fannin.
Kazalika, Keyen ya kuma nuna damuwarsa a kan yadda gwamnatin ta gaza samawar wa da musamman kananan manoma kayan aikin noma.
Shi ma shugaban masu sarrafawa da sayar da takin zamani na kasa (FEPSAN), Sadik Kassim yaba wa shirin samar da tallafin kayan aikin noma da ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci suka wanzar na shirye-shiryen aikin noma.