Kungiyar masu sarrafa fulawa ta Nijeriya (FMAN) ta ce ta samar da cibiyoyin saye da sayarwa a jihohi 13, domin kawar da dukkan hatsin da ke tattare da noman wanda ya kunshi manoma 50,000 a shekara ta 2022-2023.
Manajan na shirin bunkasa alkama na FMAN Dakta Aliyu Sama’ila ne ya bayyana haka a lokacin bikin ranar noman alkama a karamar hukumar Bunza daje jihar ta Kebbi.
- Zama Lafiya Ya Fi Zama Dan Sarki
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
Ya ce aikinsu na daya shi ne samar da kasuwa ga manoman alkama a kasar nan. “Mun noma kadada 200 na alkama a shekarar 2022, kuma yanzu mun ninka shi zuwa 400 a bana a jihar Kebbi.
Haka kuma “Muna fadada sayayyarmu a matsayin masana’antu a duk fadin jihohin da ke noman alkama ta hanyar karin ma’aikatan tarawa da karfin ajiya.
“Musamman, mun kafa cibiyoyin siyar da kayayyaki a fadin jihohin Arewa 13 don cire duk wani hatsin alkama daga manoma 50,000 a jahohin.
“Jihohin su ne Kano da Kaduna da Jigawa da Kebbi da Sakkwato da Bauchi da Adamawa da Gombe da Filato da Taraba da Zamfara da kuma Yobe.
Kazalika “Don ci gaba da fadada noman alkama a kasar nan, dole ne mu kara yawan amfanin gonakin manoma, don sanya alkama ta yi gogayya da shinkafa da sauran noman rani,” in ji Dakta Sama’ila.
Ya ce noman gonakin masu girman hekta 114 a fadin jihohin Arewa shida, domin ba da horo kan aikin noma na daga cikin shirinsu na ci gaba. Jihohin sun hada da Adamawa da Borno da Gombe da Filato da Taraba da Yobe.
“Za mu fadada shirin FMAN na kai tsaye tare da ba da lamuni don bai wa manoma 4,300 a fadin hekta 3,900 a jihohi bakwai, wato, Kano da Jigawa da Sakkwato da Kebbi da Kaduna da Binuwai da Zamfara.
“Za kuma mu fadada samar da iri tare da wasu kamfanoni shida da suka tabbatar da iri, wadanda suka hada da noman rani da damina, don samar da isasshen iri na hekta 10,000 a kakar da sauransu,” in ji shi.
Har ilayau Dakta Aliyu Samaila ya kara da cewa IMPAN ta shiga tsakani wajen siyan alkama fiye da ton 50,000 a cikin shekaru 5 da suka gabata tare da sanya hannu kan yarjejeniyar sayan kowace irin alkama da ake samu a farashi mai kyau bisa ga amfanin noma da manoman.
Bugu da kari “Mun sayi alkama kai tsaye daga sama da manoma 4,000 a cibiyoyin noman alkama 40 a cikin 2022. Ya ci gaban da cewa “Mun bayar da tallafin iri da taki da sinadarai masu amfani ga manoma 400 a shekarar 2019 da kuma manoma 700 a shekarar 2020 a jihohin Kano, Jigawa da Kebbi.
Da yake jawabi a madadin manoman, Shugaban WFAN na yankin Karamar hukumar Bunza, Alhaji Umar Abdullahi, ya yabawa FMAN kan shirin bunkasa alkama da nufin bunkasa noma a kasar nan.
Ya ce shiga tsakani da kungiyar ta yi ya baiwa manoma da dama kwarin gwiwar shiga noman alkama a jihar kebbi.
Ya kara da cewa manoman suna fuskantar sabbin dabarun noma da kuma kyawawan dabi’un noma domin bunkasa nomansu.
“Muna fatan yin hadin gwiwa tare da FMAN a duk fadin darajar don inganta yawan amfanin da muke samu ta hanyar iri masu inganci, fadada ayyukanmu, da kuma inganta hanyoyin samar da ban ruwa,” in ji Umar Abdullahi.