Wasu manoman masara a jihar Kano sun koma noman dawa sakamakon tsadar taki maimakon masara da sauran amfanin gona da suka saba yi
Wannan na dauke ne cikin wani rahoto da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya fitar, manoman a yanzu suna amfani da taki daga kashin dabbobi da sharar gida domin amfanin gona saboda karancin taki.
- Ba Zan Raga Wa ‘Yan Bindiga Ba Sai Na Ga Bayansu – Buhari
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Sace Matafiya Da Dama A Katsina
Hakazalika manoman sun koma yin noman gauraye, inda suke shuka dawa, gyada, wake ko waken soya, domin kara habaka ni’imar kasa don samun amfanin gona.
Binciken na NAN, ya nuna cewa buhun taki ya kai kimanin Naira 25,000 zuwa sama, ya danganta da nau’i da nau’in kayan.
Wani manomi mai suna Muhammad Tukur, ya ce duk shekara ya kan noma masara, amma a bana sai dawa ya shuka, saboda tsadar taki.
Tukur ya ce hakan zai ba shi damar kashe kudi kadan wajen kula da amfanin gona har zuwa lokacin girbi.
Ya kara da cewa ya yi noman gauraye, inda yake gauraya sauran amfanin gona da waken soya wadanda ba sa bukatar taki mai yawa.
Sha’anin tsadar taki abu ne dai da ya dade yana ci wa manoma tuwo a kwarya.
Sai dai gwamnatoci daga matakin tarayya zuwa jihohi sun ikirarin suna tallafawa manoman.
Amma manoma sun koka cewar tallafin ba zuwa ta hannun da ya dace, wato rijiya tana ba da ruwa, guga na hanawa ne.