Wasu daga cikin mazauna karkara a Jihar Ido, wadanda suka amfana da tallafin gwamnatin tarayya, karkashin shirin gwamnatin na inganta rayuwar kasuwancin iyali (LIFE-ND), sun bayyana yadda aikin ya inganta rayuwarsu da ta iyalansu.
Aikin wanda gidauniyar kasa da kasa ta (IFAD) ta bayar, na samar da kudi tare da hadaka da gwamnatin tarayya da kuma hukumar inganta rayuwar mazauna yankin Neja Delta (NDDC), wanda aka gudanar a yankuna uku da ke Jihar Ido.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Asibiti, Makaranta Da Gidaje Ga Al’ummar Tudun Biri – Gwamnan Kaduna
- Game Da Tambayar Nan: Ko Ka Yi Tir Da Harin Ranar 7 Ga Oktoba?
Tawagar ta IFAD da ta gwamnatin tarayya, sun kai ziyara a guraren kiwon kajin gidan gona guda goma da aka samar a yankin Ugbineh a Karamar Hukumar Obia ta Arewa maso gabas.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da aikin, wata mai kiwon kajin gidan gona, Grace Nwaozuzu ta sanar da cewa, aikin ya tsamo ta da kuma iyalanta daga cikin talauci.
Ita kuwa wata mai sana’ar kiwon kifi a yankin Uteh Efe Ehanire ta bayyana cewa, daukin da ta samu daga aikin na (LIFE-ND), ya ba ta damar kara samun sauki a cikin sana’ar tare da kara mata kwarin guiwa.
Jami’ar aikin (LIFE-ND) a jihar, Anthonia Esenwa ta sanar da cewa, tawagar ta zo jihar ne domin duba yadda ake tafiyar da kudaden da aka zuba a cikin aikin.
A nasa bangaren shugaban riko na aikin a jihar, Mista John Omoruyi ya sanar da cewa, an samar da gurare sama da 28, inda ya kara da cewa, kimanin mutane 2,250 ne a yankin Jihar Idon suka amfana da shirin.
A cewar tasa, tawagar ta ziyarci gurare uku da ake tafiyar da ayyukan daga cikin ayyuka 28 da aka gudanar a yankunan karkarara.