Daga wannan shekara da muke ciki ta 2023 zuwa 2024, gwamnatin tarayya na shirin bayar da tallafi noman rani na kimanin kashi 50 cikin 100.
Ministan aikin noma da samar da wadataccen abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyna haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar tasa ta wallafa a shafinta na sada zumunta.
- Kowacce Yarinya Za Ta Samu Ilimi Da Sana’a A Jihar Katsina – Gwamnati
- Kasafin Kuɗin 2024: A Jihar Katsina, Ɓangaren Noma Zai Samu Kashi 6.21% Kawai – Kwamishina.
Kyari ya sanar da cewa, wannan buri na daga cikin ajandar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma matakan da Gwamnatin Tinubun ke dauka, domin magance hauhawar farashin kayan masarufi a fadin kasar nan baki-daya.
A cewar Ministan, bayar da tallafin zai shafi daukacin kayan aikin noma da suka hada da Iri na noma, takin zamani da kuma maganin feshi da za a raba wa manoman.
Kazalika Ministan ya bayyana cewa, taimakon da ake samu daga wurin Bankin Raya Nahiyar Afirka (AfDB), a kan aikin noman rani na shekarar 2023 zuwa shekarar 2024, an gabatar da shi ne a karkashin shirin habaka aikin noma na (NAGS-AP).
Idan za a iya tunawa, a watan Mayun 2023 bayan an rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin cewa; gwamnatinsa ba za ta kara biyan tallafin kudin man fetur ba.