• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mansura Isah Ta Kare Kanta A Kan Neman Suna

by Rabilu Sanusi Bena
1 year ago
Mansura

Jarumar Kannywood, Mansura Isah na ci gaba da kare kanta kan zargin da wasu ke yi mata na cewa tana amfani da kasancewarta jarumar Kannywood wajen neman suna.Tana kokarin  bata wa wata makarantar firamare suna, ta bayyana cewa an yi kunbiya-kunbiya a lokacin da suka tafi asibiti domin binciken lafiyar wasu yara da ta kama suna aikata ba daidai ba a wata makarantar firamare da ke Jihar Kano.

A wani faifan bidiyo da ta fitar a kwanikin baya, Mansura Isah ta yi kira ga iyayen yara a kan su kara sa ido kan tarbiyar ‘ya’yansu, musamman ma wadanda suke fita zuwa makarantu da kasuwanni. Ta ce abin da ta gani a wata makarantar firamare ya yi matukar tayar mata da hankali.

  • Kabilar Bayankole Da Innar Amarya Ke Jima’i Da Ango Domin Gwaji
  • Ya Kamata Manchester United Ta Kori Erik ten Hag?

Mansura ta yi ikirarin ganin wasu yara kimanin su 6 suna aikata badala yayin wata ziyarar da ta kai zuwa wata makarantar firamare. Ta ce ta shiga damuwa kasancewar yaran suna da kananan shekaru.

Wadannan kalamai da ta furta ya sa hukumar Hizba tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani kwamiti domin binciken gaskiyar lamarin, jarumar ta tabbatar da cewar kwamitin da aka kafa domin binciken lamarin ya boye mata wasu daga cikin sakamakon binciken da aka yi a makarantar da kuma na asibiti.

Ta ce a lokacin da suka tafi makarantar mai yawan dalibai fiye da 6,000, daga nan aka ce dalibar da abin ya faru da ita ta fitar da wadanda suka aikata abin da ake zarginsu da aikatawa wadanda ta ce ‘yan aji 6 ne a makarantar, bayan ta fitar da su, sai suka dunguma zuwa asibiti domin gwajin lafiyarsu.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Bayan sun tafi asibitin tare da sauran ‘yan kwamitin, sai aka shiga da su dakin gwaji, inda ita kuma aka hana ta shiga. Bayan an kammala gwajin lafiyarsu, an hana ta ganin takardar sakamakon gwajin lafiyar da aka yi masu duk da cewa ya kamata a yi hakan kamar yadda Mansura ta tabbatar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
Nishadi

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Next Post
Rahama Sadau: Daga Jarumar Kannywood Ta Zama Jarumar Bollywood

Rahama Sadau: Daga Jarumar Kannywood Ta Zama Jarumar Bollywood

LABARAI MASU NASABA

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Mansura

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.