An sanar da cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sanu nasarar lashe zaben kamar yadda shugaba hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar.
Tinubu Ya samu nasarar ce da kuri’a 8,794,726, sai Atiku Abubakar dan takarar PDP,yana da kuei’a 6,984,520. Sai na uku Peter Obi na LP mai kuri’a 6,101,533 sai Rabi’u Kwankwaso na NNPP ya samu kuri’u 1,496,687.
Shirin da aka yi wa zaben, an sa rai sosai, yadda ‘yan takarar shugaban kasar guda hudu kowanne zai samu sakamakonsa na dukkan jihohi 36 da na Abuja.
An ci karo da wasu matsaloli wadanda dama ana tunaninsu na tattara sakamakon zaben wasu mazabu.
Peter Obi ya samu nasara a mazabu tara da ke fadar shugaban kasa Abuja da kuri’a 499 sai Tinubu ya samu 184 sai Atiku mai 142.
Sai kuma inda Obi ya samu nasara a karamar hukumar Ikeja, karamar hukumar da Tinubu ya fito.
Obi ya kada Tinubu da kuri’a 582,454, inda ya samu 572, 606 botes shi kuma Atiku ya tsira da kuri’a 75,750.
Haka ma Obi ya lashe Nasarawa da wasu jihohin Arewa kamar Kaduna da jihar Filato.
A Nasarawa, Obi ya samu 191,361 inda Tinubu, ya samu 172,922 sai kuma Atiku ya samu 147,093.
Sai jihar Delta inda Obi ya lashe zaben da kuri’a 341,866 sai Atiku ya samu 161,600 yayin da Tinubu ya samu kuri’a 90,183.
Atiku ya lashe zabe a Katsina jihar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuri’a 489,045 yayin da Tinubu ya samu 482,283.
Shugan jam’iyyar APC Abdullahi Adamu, ya fadi a mazabarsa yayin da LP ta samu nasara da kuri’a 132 sai Tinubu na APC ya samu 85.
El-Rufai bai sau nasara ba a karamar hukumarsa ba. A Zariya kuwa shi da dan takarar gwamna Uba Sani Atiku ya samu nasara a kansu da kuri’a 62,260 wanda ya kayar da Tinubu mai kuri’a 41,432. Sai Kwankwaso na NNPP ya samu 8,729 yayin da Obi ya samu kuri’a 3,634.
Gaba daya kuma, Atiku ya samu nasara a Kaduna da kuri’a 554,360 sai Tinubu, ya samu 399,293 shi kuwa Obi kuri’a 294,494 ya samu.
Atiku ya samu nasara kananan hukumomi 14, Obi ya samu kananan hukumomi bakwai sai Tinubu wanda ya samu kananan hukumomi biyu. Tinubu ya samu nasara a kan Obi,da Atiku a Ribas.