‘Yan majalisar tarayya da suka yi hutun makwanni biyu, sun ci gaba da zama a ranar Talata 4 ga watan Yuli don fara aikin majalisa gadan-gadan.
Majalisar dattawa da ta wakilai dai sun dage zama bayan ‘yan kwanaki da rantsar da sabbin shugabanninsu har zuwa ranar 4 ga watan Yuli domin samun damar ba da mukamai da ofisoshi ga masu dawowa da kuma sabbin ‘yan majalisa.
- Bukatar Dakatar Da Kara Kudin Wutar Lantarki A Nijeriya
- Kamfanin Meta Mamallakin Facebook Ya Yi Wa Twitter Kishiya
Kafin tafiya hutun, majalisun biyu sun zauna a takaice bayan an gudanar da zabukan da aka fafata. A zaben da aka yi na shugabannin majalisar ta 10, ’yan takarar jam’iyyar APC ne suka samu nasara duk da barazanar da wasu ‘ya`yan jam’iyyar da na ‘yan adawa suka yi cewa ba za su amince da dauki-dora ba.
A bangare zauren majalisar wakilai kuwa, Hon. Tajudeen Abass daga Jihar Kaduna da Hon. Benjamin Kalu daga Jihar Abiya ne suka yi nasara a matsayin shugaban majalisar wakilai da mataimaki.
Yayin da suke shirin bude sabon babi na zaman majalisan bayan dawowa daga hutu, ana sa rai za su yi aiki tukuru wajen tunkarar muhimman batutuwan da suka shafi kasa da wasu ayyukan da ba a kammala ba. Abu na farko da majalisun biyu suka yi shi ne sanar da wadanda za su taya su gudanar da aikin majalisar a mukamai daban-daban.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana sunayen wadanda aka nada a manyan mukamai na majalisar dattawa ta 10.
Daga cikin wadanda aka nada sun hada da Sanata Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar. Bamidele na wakiltar Ekiti ta tsakiya a majalisar dattawa. Sauran sun hada da Sanata Dabid Umahi mai wakiltar Ebonyi ta Kudu a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.
Ya yin da Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya zama mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Sanata Lola Ashiru, mai wakiltar Kwara ta Kudu a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.
Akpabio ya ce an nada su a mukaman ne bisa yarjejeniya.
Hakazalika, a zauren majalisar wakilai, shugaban majalisar Tajudeen Abbas ya sanar da Julius Ihonbbere daga Jihar Edo a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar da kuma Usman Kumo daga Jihar Gombe a matsayin mai tsawatarwa na majalisar.
Abbas ya kuma bayyana Halims Abdulahi daga Kogi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye da Oriyomi Onanuga daga Ogun a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.
Kingsley Chinda daga Jihar Ribas shi ne aka ba shugaban marasa rinjaye, sai Ali Isah daga Jihar Gombe a matsayin mai tsawatarwa na marasa rinjaye da Madaki Aliyu daga Jihar Kano a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye da George Adegeye daga Jihar Legas da ya zama mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Sai dai kuma, kamar tsugune ba ta kare ba, saboda jam’iyyar APC mai mulki ta nesanta kanta da wannan zabi na wadanda aka bai wa mukamai a majalisar, a hannu guda kuma gwamnonin jam’iyyar suka ce suna goyon bayan shugabannin majalisar kan zabinsu. Ba a dai san yadda za ta kaya ba sai nan gaba.
A halin da ake ciki kuma, akwai babban jan aiki da ke gaban majalisun musamman ta fuskar nada kwamitoci da shugabanninsu:
- Rikicin Shugabancin Kwamitoci
Ana sa ran shugabannin majalisun guda biyu za su bayyana shugabanni da mambobin kwamitoci. Akwai rahotannin ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan majalisar kan neman shugabanci da mambobin kwamitoci.
Haka kuma manyan ‘yan majalisa suna fafutukar neman samun kwamitoci masu gwabi da mukamai da suka fi daraja.
A daidai lokacin da aka zabi shugaban majalisar dattawa, Akpabio daga yankin kudu maso kudu, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau daga yankin Arewa maso yamma, shugaban majalisar wakilai, Abbas daga yankin Arewa maso yamma da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Kalu daga yankin Kudu maso gabas, ’yan majalisa daga wasu shiyyoyi musamman Arewa maso gabas da Arewa ta tsakiya na kokawa kan ba su kananan mukamai a zauren majalisun. A halin yanzu an mayar da hankali a ga su wane ne za a nada a kwamitoci masu tsoka wadanda za su yi aiki a bangaren mai da kudade da sauran harkokin tattalin arziki, sannan su wane ne za a bari da fafutuka a kwamitocin sassan da ba su da maiko.
- Batun Rashin Tsaro Da Tabbatar Da Nadin Shugabannin Hafsoshin Tsaro
A majalissar da ta gabata, batutuwan da suka shafi tsaro a ko da yaushe su ne ginshikin abubuwan da ake tattauwa a zauren majalisar dattawa da na wakilai, saboda wasu kudurori da suka shafi tsaro da ‘yan majalisar suka yi.
Sai dai kuma a yanzu tsaron kasar na kara tabarbarewa a kowace rana saboda sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa a arewa maso gabas da arewa maso yamma har ma da kudu maso yamma. Ana sa ran majalisar dokokin kasar ta 10 za ta fito da wasu dabaru da za su taimaka wa bangaren zartarwa na gwamnati wajen dakile matsalar rashin tsaro.
Ana sa ran ‘yan majalisar tarayya za su ci gaba da tantance sabbin shugabannin hafsoshin tsaro da sufeto janar na ‘yansanda da kuma shugaban hukumar kwastam da Shugaba Bola Tinubu ya nada kwanan nan.
Wadanda aka nada za su ci gaba da yin aiki ne a kan mukamansu, har sai majalisar dokokin kasar ta tabbatar da su. Za su bayyana a gaban kwamitin tsaro lokacin da aka kafa.
Sanatocin da za su ci gaba da zama kuma za su tantance wadanda aka nada a matsayin ministoci da zarar an mika sunayensu ga majalisar dattawa domin tabbatar da su.
- Ajandar Majalisun
Ana sa ran dukkan majalisun biyu za su bayyana ajandodinsu, inda za su bayyana abubuwan da za su fi ba da muhimmanci wanda za su mayar da hankali a cikin shekaru hudu masu zuwa.
Shugaban majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, a jawabinsa na ranar kaddamar da majalisar ya ce a karkashinsa, majalisa ta 10 za ta dora har ta zarce nasarorin da aka samu a zauren majalisa ta 9.
Ya ce majalisar ta 10 za ta gabatar da gyare-gyare da sabbin abubuwa don amfanin ‘yan Nijeriya. Ya kara da cewa nan da ‘yan makonni kadan, sabuwar majalisar wakilai za ta fitar da ajandarta da ta tsara.
Ana sa ran shugabannin ba za su yi kasa a gwiwa ba. Ana tsammani zauren majalisun na 10 su kasance ba a taba samun irinsu ba a tarihin majalisar Nijeriya.