Bayan samun amincewar majalisar gudanarwar kasar Sin, babban bankin kasar Sin da babban bankin Nijeriya sun sabunta yarjejeniyarsu a kan musayar kudaden kasashensu da jimillarsu ta kai RMB yuan biliyan 15 ko kuma kudin Nijeriya kimanin Naira tiriliyan 3 da biliyan 280.
Yarjejeniyar wacce aka cimma a kwanan nan, za ta yi aiki na tsawon shekaru uku, kuma akwai damar kara mata wa’adi bisa sahalewar kasashen biyu.
Sabunta yarjejeniyar musayar kudin a tsakanin Sin da Nijeriya zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwar sashen kudi, tare da fadada amfani da kudin kasa a cikin gida tsakanin Sin da Nijeriya, kana zai habaka harkokin cinikayya da zuba jari tsakanin sassan biyu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)