Yayin da shekara ta 2024 ta kare, ‘yan Nijeriya sun ci karo da dimbin al’amuran siyasa da suka dabayyaye bangaren siyasar kasar a 2024. Tun daga sauye-sauyen siyasa zuwa fuskar diflomasiyya, ga wasu daga cikin manyan batutuwa 10 da suka mamaye siyasar Nijeriya a 2024 kamar haka:
Amincewa Da Sabon Taken Kasa
A wani yunkuri na inganta hadin kan kasa da kuma sanin manufofin kasar, gwamnatin Nijeriya ta maido da tsohon taken kasar na asali, wanda ake amfani da ita tun daga 1960 zuwa 1978.
- Dubun Wata Budurwa Da Wasu 5 Ya Cika Bayan Ta Sace Wayoyin Salula 30 Na Matan Aure A Kano
- Takardun Kuɗi Sun Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 4.8 Duk Da Ƙarancin Kuɗi A Nijeriya
Karin Mafi Karancin Albashi
Gwamnati ta kara mafi karancin albashi na kasa daga naira 30,000 zuwa naira 70,000 a matsayin martani ga tsadar rayuwa. Wannan shawarar ta biyo bayan tsawaita tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago da jami’an gwamnati.
Lalacewar Babban Tashar Wutar Lantarki
Rugujewar tashar wutar lantarki ta kasa ta nuna irin kalubalen da ake fuskanta a fannin samar da wutar lantarki a Nijeriya, wanda ke kawo cikas ga rayuwar yau da kullum ga miliyoyin ‘yan Nijeriya.
Gudanar Da Zanga-zangar Kamar Gwamnati Mara Kyau
Zanga-zangar dai ta barke a fadin kasar nan a cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa da kunci, lamarin da ‘yan Nijeriya suka dora alhakinsa kan sabbin sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi. Akalla mutane 11 aka kashe, sannan an kama dan jarida daya.
Garambawul Ga Majalisar Manistoci
Shugaba Tinubu ya aiwatar da garambawul a majalisar ministocinsa, inda ya kori ministocin ilimi, yawon shakatawa, harkokin mata, da ci gaban matasa, da karamar ministar gidaje.
Zaben Shugaban Kasan Amurka
Zaben shugaban kasar Amurka na 2024 ya jawo hankulan ‘yan Nijeriya matuka, musamman saboda tasirin da manufofin ‘yan takara za su yi a Nijeriya.
Fashewar Bam A Ibadan
Wani abun fashewa da aka yi a garin Ibadan na Jihar Oyo, ya nuna baraka kan al’amuran tsaro, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama da kuma jikkata mutane masu dimbin yawa.
Garkuwa Da Daliban Kuriga
An yi garkuwa da dalibai sama da 200 da wani malami a garin Kuriga da ke Jihar Kaduna, amma daga baya aka sako su.
Turmutsutsun Rabon Kayan Tallafi A Ibadan Da Anambra Da Abuja
An samu turmutsutsu wajen rabon kayan tallafin Kirsimeti a Ibadan da Jihar Anambra da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda ya haifar da hasarar rayuka da jikkatar jama’a da dama, lamarin da ke nuna bukatar inganta matakan dakile cunkoson jama’a da kuma tsarin bayar da tallafin kayan abinci ko na kudi ko kuma na agajin gaggawa.