Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, a ranar Alhamis ya bada sanarwar wani gagarumin shiri na Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, wanda ya bada damar karɓar albashi har ƙarshen rayuwa ga duk wani babban jami’i da ya yi ritaya daga ma’aikatar a matsayin Mataimakin Kwanturola, Kwanturola, ko Kwamanda-Janar zuwa sama.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Babban Taron Bita na Ministan na shekarar 2025 a Abuja, inda ya bayyana nasarorin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida tare da nanata sadaukarwar ta ga aiwatar da sauye-sauye da ƙarfafa wa ma’aikata gwiwa a hukumomin da ke ƙarƙashin ta.
- AC Milan Ta Amince Da Biyan Yuro Miliyan 36 Domin Daukar Nkunku Daga Chelsea
- Shugaban NPA, Dantsoho Ya Zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Tashoshin Ruwa Ta Duniya
Hukumomin da za su amfana da wannan tsari a ma’aikatar su ne: Hukumar Gyaran Hali (wato ta gidajen yari), Hukumar Shige-da-Fice (NIS), Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya(FFS), da Hukumar Tsaro ta farin kaya (NSCDC).
Wannan bayani yana ƙunshe ne a cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na Ƙasa (PRO) na Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, DCF P.O. Abraham, ya fitar jim kaɗan bayan taron bitar.
Ya ce: “Ministan ya bayyana matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu bisa ga ɗimbin goyon bayan sa, yana mai tabbatar da cewa dukkan hukumomin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida suna amfana da albarkatun da ke cikin Shirin Sabunta Fata.”
Tunji-Ojo ya ci gaba da lissafa manyan nasarorin ma’aikatar, waɗanda suka haɗa da kammala aikin ƙarin girman ma’aikata wanda aka daɗe ba a yi ba, ya ce sama da ma’aikata 50,000 ne aka yi wa ƙarin girma a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Haka kuma ya ce daga yanzu ba za a riƙa yin ƙarin girma bisa matakin daɗewa a aiki ba, sai dai bisa iya aiki da kuma dagewa, ya nanata cewa ma’aikatar ta ƙudiri aniyar yi wa kowane ma’aikaci sakayya bisa ga ƙoƙarin da ya yi a aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp