• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Jami’an Jam’iyyun Duniya Da Abokan Kasar Sin Sun Taya Murnar Bude Taron Wakilan JKS Karo Na 20

by CMG Hausa
3 years ago
JKS

Yayin da ake gudanar da taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20, manyan jami’an jam’iyyun siyasa a sassan duniya, da abokan kasar Sin sun aika da sakwanni ga kwamitin tsakiya na JKS da babban sakataren JKS Xi Jinping, don taya murnar bude babban taron wakilan JKS karo na 20.

Shugaban jam’iyyar ANC ta kasar Afirka ta Kudu kuma shugaban kasar Matamela Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, ana gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20 a lokaci mai muhimmanci da kasar Sin da ma duniya ke tinkarar manyan sauye-sauye.

  • An Bude Babban Taron Wakilan JKS Karo Na 20

Jam’iyyar ANC tana dora muhimmanci sosai kan sada zumunta dake tsakaninta da jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma hadin gwiwa da burinsu iri daya, su ne tushe na kiyaye dangantakar dake tsakanin jam’iyyun biyu. Yayin da ake tinkarar sauye-sauyen da duniya fama da su, ya yi imanin cewa, jam’iyyun biyu za su yi amfani da dama da ma tinkarar kalubale tare, don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin jam’iyyun biyu.

Kana ya yi fatan za a cimma nasarar gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20, da fatan za a samu muhimman sakamako a yayin taron, ta yadda hakan zai kai ga bunkasar jam’iyyar Kwaminis ta Sin tare da cimma burin da ta sanya gaba na samun wadata a kasar Sin baki daya.

Shi ma shugaban kasar Gabon Ali-Ben Bongo Ondimba ya taya murnar bude babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara, tare da yin imani da cewa, za a tsai da kudurori masu dacewa a yayin taron.

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Ya kara da cewa, bisa jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, wadda ta kawowa jama’arta zaman lafiya da kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa, don haka, ya jinjinawa jam’iyyar Kwaminis ta Sin bisa ga muhimmiyar rawa da take takawa game da harkokin da suka shafi kasar Sin baki daya. (Zainab)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
Atiku Ya Yi Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Da Sake Farfado Da Masana’antu A Jihar Kaduna

Atiku Ya Yi Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Da Sake Farfado Da Masana'antu A Jihar Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo

Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5

November 10, 2025
Matatun mai

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

November 10, 2025
Jibrin Kofa

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

November 10, 2025
Boko haram

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.