Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya sha alwashin dawo da zaman lafiya tare da farfado da masana’antun da suka mutu a jihar Kaduna idan har ya zama shugaban Nijeriya a 2023.
Atikun ya kuma yi alkawarin gyara hanyoyin da suka hada Kaduna da Kano; Kaduna da Jos da kuma Kaduna da Abuja.
- Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Kan Magoya Bayan PDP A Jihar Kaduna
- Na Amince Zan Goyi Bayan Takarar Atiku Abubakar —Wike
Atiku, wanda ya bayyana hakan a yayin taron gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Kaduna, ya ce: “Da farko, bari na yi maku godiya da irin goyon bayan da kuka ba ni a 2019,”
“Jihar Kaduna ta ba ni kuri’u mafi yawa a Nijeriya. Na zo nan ne domin in yi alkawari a madadin jam’iyyar PDP cewa idan kun ba mu kuri’un ku, za mu dawo da zaman lafiya a Jihar Kaduna. Za a magance matsalolin tsaro,”
“Mun yi alkawarin za mu sake farfado da masana’antu a jihar Kaduna tare da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu a jihar Kaduna,”
“Za mu kafa wadancan masana’antu. Muna muku alƙawarin cewa hanyar da ta haɗa Kaduna da Kano, ta haɗa Kaduna zuwa Jos, ta haɗa Kaduna da Abuja, da yardar Allah za ta ƙare. Wadannan ayyuka guda hudu karkashin jam’iyyar PDP idan kun zabi PDP,” in ji Atiku.