Goruba, a turance ana kiranta da Doum palm fruits an kuma hakikance cewa, goruba, ta samu asali ne daga kasar Masar, amma a yanzu ana iya shuka ta a gurare da dama, ciki har da Nijeriya.
Goruba na yin bishiya ne, inda ake tsinkar ‘ya’yanta domin ci, ko kuma a sarrafa ta zuwa wani naucin abinci.
- Sojoji Sun Cafke ‘Yan Bindiga 7, Sun Kubutar Da Wasu Mutane
- Da Ɗumi-ɗuminsa: Kwamishina Bunkasa Kasuwanci Da Masana’antu Na Jigawa Ya Rasu
Manyan Kasuwannin Da Aka Fi Samun Goruba A Nijeriya:
Ana samun goruba a kasuwar Gamboru da ke cikin garin Maiduguri a jihar Borno, inda a wannan kasuwar ake zuwa ana siyenta da yawa domin yin safararta zuwa wasu jihohin kasar nan.
Bugu da kari, akwai kuma wasu manyan kasuwannin a kasar nan da ake yin hadahadar kasuwancin goruba.
Ana Hada-hadar Kasuwancin Goruba A Wasu kananan Kasuwanni:
A wasu kananan kasuwannin da ke fadin kasar nan, ana yin hada-hadar kasuwancin goruba, domin mutane da dama, ciki har da manyan mutane suna zuwa domin su siya.
Haka su ma yara suna siyen busasshiyar goruba domin ci, wasu kuma yaran na siyenta domin tafiya da ita makaranta don ci ganin cewa tana taimaka musu kamar abinci.
Ana samun goruba a kasuwannin unguwani da ke cikin gari ko kuma a wasu shaguna haka wasu su kan yi tallarta a kan hanya.
A yankin Arewa maso gabas, da ke cikin kasar nan, Allah ya albarkaci yankin da goruba mai yawa.
Goruba na da dandano mai dadi, musamman mutanen da ke zaune a yankunan da ke da zafi, suna yin amfani da goruba, ganin, tana taimaka wa yanayin jikin ‘yan’adam.
Ana Sarrafata Wajen Hada Abinci:
Ana sarrafa goruba wajen hada ta a cikin abinci, ta hanyar saka ta a cikin ruwa ko kuma a cikin ruwan zafi har zuwa wasu ‘yan mintuna, ganin cewa, tana dauke da sinadaran da ke gina jikin ‘yan’adam.
Har ila yau, ana sarrafa goruba wajen hada shayi, haka ana sarrafa goruba wajen yin kayan lemon Kwalba don a samu dandano.
Amfanin Goruba Ga Kiwon Lafiyar ‘Yan’adam:
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, goruba na taimaka wa kiwon lafiyar ‘yan’adam, musamman ganin cewa, tana da sinadarin fiber, haka kuma tana taimaka wa wajen rage karfin ciwon suga.
Bugu da kari, busasshiyar goruba na taimaka wa musu fama da ciwon suga da saurin narkar da abincin da mutun ya ci, haka tana dauke da sinadarin carbohydrate da kuma bitamins B.
Har ila yau, masu ilimi a fannin kiwon lafiya sun yi ittafakin cewa, goruba na taimaka wa wajen kara bunkasa aikin kwakwalwar ’yan’adam.
Goruba dai, na girma a jikin bishiya inda wasu ki ciro danyarta don su busar da ita, wasu kuma ke barinta a jikin bishiyar sai ta bushe da kanta kafin su cire ta.