Pierre Emeric Aubameyang ya kammala komawa kungiyar kwallon kafa ta Olympique Marseille da ke kasar Faransa.
Dan wasan Gabon, mai shekaru 34, ya ci kwallaye uku kacal a wasanni 22 da ya buga wa Chelsea, bayan da ya koma daga Barcelona kan kudi fam miliyan 10.3 a watan Satumban da ta gabata.
- Rusau: Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano Naira Miliyan 2
- Hajjin 2023: NAHCON Za Ta Kammala Dawo Da Alhazan Nijeriya A Watan Agusta
Babu wata shaida da ta bayyana ko Marseille ta biya kudin dan wasan wanda haifaffen Faransa ne.
Aubameyang ya fice daga gasar Firimiyar Ingila a karo na biyu cikin watanni 18, bayan ya shafe shekaru hudu a Arsenal daga 2018 kafin ya koma Barcelona a watan Janairun 2022.
Ya zura kwallaye 13 a wasanni 23 a cikin watanni shida da ya yi a Barcelona, amma ya kasa tabuka abin azo a gani a Stamford Bridge.
Gwarzon dan kwallon Afrika na 2015, ya buga wasa daya kacal a karkashin Thomas Tuchel, tsohon kocinsa a Borussia Dortmund, kafin a kore shi tare da maye gurbinsa da Graham Potter.
Kwallaye uku a wasanni uku da ya buga a watan Oktoba ya nuna yiwuwar dawowa fagen daga, amma Aubameyang ya kasa sake zura kwallo a raga.
An cire shi daga cikin ‘yan wasan da za su buga gasar zakarun Turai a gasar cin kofin zakarun Turai bayan da aka sayo sabbin ‘yan wasa a watan Janairu, ciki har da ‘yan wasan gaba Mykhailo Mudryk da Noni Madueke.
Aubameyang ya koma gasar Ligue 1 ta kasar Faransa bayan barinta shekaru 10 da suka gabata, inda ya lashe Coupe de la Ligue a 2013 a Monaco.
Aubameyang shi ne dan wasan Chelsea na bakwai da ya bar kungiyar a bana.
Dan wasan tsakiya na Croatia Mateo Kovacic ya koma Manchester City, Kai Havertz ya koma Arsenal sannan Mason Mount ya koma Manchester United, yayin da mai tsaron gida Edouard Mendy da mai tsaron baya Kalidou Koulibaly suka koma kungiyar Al-Ahli ta Saudiyya.
N’Golo Kante ya koma Saudiyya, inda ya koma Al-Ittihad, yayin da ‘yan wasan tsakiya Ruben Loftus-Cheek da Christian Pulisic suka koma AC Milan, shi kuma kyaftin din Cesar Azpilicueta ya koma Atletico Madrid.
Blues ta sayi dan wasan gaba na Brazil Angelo Gabriel, mai shekara 18 daga Santos, dan wasan Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 25, daga RB Leipzig, da dan wasan Senegal Nicolas Jackson mai shekara 22 daga Villarreal.