Tun daga lokacin da tauraron ci gaban kasar Sin ya fara haskawa a duniya, an rika shafa wa kasar bakin fenti domin dakile ci gabanta da kuma hana ta zama mai taka muhimmiyar rawa a fagen kasa da kasa. Sai dai, sannu a hankali gaskiya na ci gaba da bayyana, inda hakan ya sa kima da martabar kasar ke karuwa a idanun duniya.
Gudunmawar Sin a fagen samar da kwanciyar hankali a duniya a bisa turbar Majalisar Dinkin Duniya, da zama kasa mafi zuba jari a bangaren makamashi mai tsafta da rage fitar da hayaki mai gurbata yanayi, da kuma huldodin kawance na bunkasa tattalin arziki da kasashe daban-daban, ta kawar da dodoridon da maha’inta ke yi.
Idan ba a manta ba, wata kididdigar da cibiyar bincike ta Pew ta fitar tare da wallafawa a watan Yulin bana, ta nuna cewa, martabar kasar Sin a idanun mutanen duniya ta karu a cikin kasashe 15 daga cikin 25 da aka yi nazari a kansu, idan aka kwatanta da bara. Kazalika, a cikin kasashe 16, an kara amincewa da hikimomi da shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar wa duniya domin ba da gudunmawar kasar Sin ga kyautata tafiyar da harkokin duniya. Duk da cewa, ana nuna shakku a yawancin kasashe masu sukuni, amma kasashe masu tasowa da raunana na ci gaba da nuna amincewa sosai, har ma galibi suna ambaton rawar da kasar Sin take takawa a matsayin amintacciyar abokiyar tattalin arziki da kuma karuwar tasirinta a harkokin cinikayya da kayayyakin more rayuwa.
Bugu da kari, kididdigar da aka gudanar a kan yadda ’yan kasar Sin ke kallon rawar da kasar ke takawa a duniya, watau CCGPS, wadda aka wallafa a watan Yunin 2025, ta bayyana goyon bayan al’ummar kasar mai karfi ga kara himmar kasar a fagen huldar diflomasiyya har ma da bangaren soja, tare da amfani da dabaru mafi dacewa wajen taimakawa magance kalubalen siyasar yankuna. Wannan ya nuna cewa, Sin tana tafiya a kan turbar da ta dace wajen sauke nauyinta a matsayinta na babbar kasa.
Kasashen duniya sun gaji da masu fakewa da sunan dimokuradiyya da ’yanci suna cimma boyayyun manufofinsu na haddasa yaki domin sayar da makamansu, da kakaba takunkumai masu tagayyara rayukan al’ummun kasashe, da neman yin babakere a siyasar yankuna maimakon hadin gwiwa bisa gaskiya da adalci.
Kasar Sin ba ta boye manufofinta na hulda da kasashen waje, wadanda ta kafa su a turbar hadin gwiwar moriyar juna, da zuba jari a bangaren ababen more rayuwa da kuma karfafa daukar mataki na bai-daya wajen shawo kan manyan kalubalen duniya kamar na sauyin yanayi da kuma yaki da talauci, inda take aiwatar da su a aikace ba da fatar baki ba. Su kuma masu fakewa da guzuma don su harbi karsana, mutuncinsu ya shiga “kila-wa-kala”, domin dama an ce, “mutunci madara ne, idan ya zube ba ya kwasuwa duka!” (Abdulrazaq Yahuza Jere)














