A halin da ake ciki kuma, Babban Hafsan Sojojin Kasa na Nijeriya, Laftanal Janar Farouk Yahaya a wani martani da ya mayar kan ta’asar da ‘yan ta’adda da sauran masu daukar makami suke yi a kasar nan, ya bayyana cewa karshensu ya zo.
Ya yi wannan gargadin ne a yayin da ya ziyarci Maiduguri domin kara zaburad da sojojin da ke fatattakar ‘yan ta’addan boko haram da kuma kaddamar da wasu manyan ayyuka na ci gaba da aka aiwatar domin kyautata jin dadin sojojin da ke fagen daga.
Buhari Ya Gaji, Ya Kamata Ya Koma Gida Ya Huta Kawai – Elumelu
“Wannan sako ne ga dukkan masu aikata miyagun laifuka, walau suna tsara bidiyo su watsa ko ma dai me suke yi, karshensu ya zo kuma za mu cimma su da yardar Allah.”
Laftanar Janar Yahaya ya yi gargadin ne a ranar Litinin inda ya kara da cewa, ‘yan fashin daji, da ‘yan boko haram da sauran masu aikata miyagun laifuka ba za su tsira ba, kana ya yi alkawarin cewa babu wanda zai samu mabuya a cikinsu.
Wazalika Babban Hafsan Sojin ya ce duk wani mutum da yake daukar makami don ya yaki Nijeriya a kan kowane irin dalili ya shirya fuskantar fushin doka.