Daya daga cikin iyaye mata da ke harkar fim wadanda kuma suka shafe shekara da shekaru a wannan masana’antar ta Kannywood ana damawa dasu Maryam Suleiman ko kuma Maryam CTV kamar yadda akafi saninta ta bayyana cewar babban abinda ke ci mata tuwo a kwarya a masana’antar Kannywood shi ne yadda ake ajiye al’adar Malam Bahaushe da dabi’unsa a cikin fina-finai a dauko wasu al’adun daban na kasashen ketare kuma duk da cewar da harshen Hausa ake amfani wajen yin fim din.
Maryam a wata hira da ta yi da jaruma Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’ ta nuna rashin jin dadinta dangane da wannan halayya ta masu daukar nauyin shirya fina-finan Hausa da kuma sauran batutuwa da aka tabo.
- Kyawawan Dabi’u Da Hasken Sanin Allah, Halittar Annabawa Ce Ba Koya Suke Ba
- Jarumin Bollywood Saif Ali Khan Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Tunda farko dai Maryam ta warware zare da abawa a kan takaddamar da akeyi dangane da inda ta samo wannan suna na CTB inda ta ce ba wani abu bane ya sa ake kiranta da wannan suna illa saboda ta dade tana aiki a wannan ma’iakar Talabijin ta CTB kafin ta shigo cikin harkar Kannywood gadan-gadan.
Ta ci gaba da cewa akwai batutuwa da dama da ya kamata ace an yi duba akansu a wannan masana’anta tamu mai albarka ta Kannywood muddin ana son ci gabanta,daga ciki akwai samar da takardar yarjejeniya da ya kamata masu shirya fina-finai da jarumai za su dinga sakawa hannu a gaban shaidu dangane da abinda mai shirya fim zai biya jarumi tun kafin ma a fara aiki.
Ba wani abu ya sa nace haka ba illa saboda a tunanina wannan wata hanya ce da zata saukaka ma dukkan bangarorin biyu wato furodusa da jarumi, idan wannan abu ya tabbata zai zamana cewar akwai tsari wajen biyan kudin aiki tsakanin furodusa da jarumi don kuwa ko a addinin musulunci akwai batun yarjejeniyar kasuwanci a duk lokacin da za a kulla kasuwanci in jita.
Maryam Suleiman wadda tace tun kafin a kafa wannan masana’antar ta Kannywood ta ke harkar fim ta ci gaba da cewar ni aikin nan ba bakon abu ba ne a wajena domin kuwa tun ana bani Naira 150 a matsayin albashin wata nike yin aikin wasan kwaikwayo amma yanzu sai kaga wai mutum ne zai dauke ka aiki amma ya kasa biyanka hakkinka na kudi ko bayan an kammala wannan aikin.
Hakan ya taba faruwa dani wata rana na yi wa wani furodusa aiki sai aka dauki tsawon lokaci ba tare da wannan mutumin ya biyani kudin aiki na ba, wata rana muka hadu dashi sai nike masa wasa ina cewa zan samu kudina anan Duniya ko sai mun je Lahira sai mutumin ya buda baki ya ce sai dai idan munje can Lahira sai ya bani, wannan maganar ta matukar daga mani hankali domin ban yi tunanin maganar ta fito daga bakin wannan mutumin ba.
Daga karshe ta yi kira ga jarumai musamman mata masu tasowa da su tabbatar sun koyi halaye irin na wadanda suke kallo a matsayin abin koyi a wajensu a cikin masana’antar Kannywood (Role Model), ga misali idan kina so ki zama kamar Hadiza Gabon to dole ne ki yi biyayya da jajircewa kamar yadda Hadiza Gabon ke yi hakazalika idan kinaso ki zama kamar Rahama Sadau dole ne kiyi aiki tukuru kamar yadda itama Rahama Sadau ta yi.