Masana harkokin tsaro da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma wadanda ta’addancin ya shafa, sun bayyana rashin jin dadinsu na yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka koma cikin al’umma, don ci gaba da gudanar da rayuwarsu; ba tare da la’akari da wadanda suka sanya cikin halin ha’ula’i ba.
An zargi gwamnatin kasar da yi wa tubabbun ’yan kungiyar goma ta arziki, yayin da kuma wadanda zalincin nasu ya shafa ke cikin kunci a sansanoninsu na ‘yan gudun hijira da ke fadin wannan kasa.
Wani mai ba da shawara a kan harkokin tsaro, Abdullahi Mohammed Jabi, ya caccaki yadda aka dawo da tubabbun ‘yan ta’addan su kimanin 5000, cikin al’ummar da suka tava kai wa hare-haren ta’addanci.
- Babu Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Tsarinmu – Gwamnan Zamfara
- Dogaro Da Kasashen Yamma Ba Zai Tabbatar Da Tsaro A Philippines Ba
Ya ce, wannan matakin da aka dauka ya kawo cikas ga sadaukarwar da ‘yan Nijeriya masu kishin kasa suka yi, wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen kare kasar.
A baya-bayan nan dai, an kashe sojojin kasar kimanin 22; ciki har da kwamanda a Borno, a ranar 25 ga watan Janairun 2025, a wani farmaki da suka kai wa ‘yan ta’addan a wani waje da ake kira ‘Timbuktu Triangle’, bayan ‘yan ta’addan sun baza ‘yan kunar-bakin-wake a cikin motoci dauke da bamabamai, don kakkave sojojin.
Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu.
Haka nan, ya kuma sake bayyana hadewar komawar tasu cikin al’umma a matsayin wani babban kuskure wajen aiwatar da manufofin da suka dace.
Ya kara da cewa, “Abin da ya kamata mu yi wa ‘yan ta’adda shi ne, mu tabbata sun girbi abin da suka shuka. Saboda haka, idan har da gaske muke wajen kawar da ta’addanci a fadin wannan kasa, ya kamata mu sanya ido yadda ya kamata. Bana goyon bayan wannan abu da ake kira; sake shigar da ‘yan ta’adda cikin al’umma da siyasa.
“Wannan ba daidai ba ne, kuskure ne. Wadannan mutane, babu wani ci gaba da za su kawo wa kasa ko al’ummar da ke cikinta, in ban da kara dagula al’amura da za su yi”, a cewarsa.
Jabi ya ci gaba da cewa, sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda, manoman da ya kamata a ce suna samar wa al’umma abinci; suna can sansanonin ‘yan gudun hijira suna rayuwa cikin mawuyacin hali.
Wani dan asalin Jihar Yobe, wanda ba ya so a bayyana sunansa, saboda fargabar ramuwar gayya; ya nuna rashin jin dadinsa ga gwamnatin tarayya da na jihohi, dangane da shirin sake dawo da wadannan ‘yan ta’adda cikin al’umma.
Ya ce, kyautuwa ya yi gwamnatin tarayya a ce tuni ta kammala fatattakar wadannan ‘yan ta’adda, kafin ta kai ga fara aiwatar da wannan shi.
Shi ma a nasa vangaren, babban daraktan cibiyar kare hakkin al’umma (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani ya ce, mayar da ‘yan ta’addan da suka tuba, ba tare da sake tsugunar da wadanda ta’addacin ya shafa ba, abu ne da zai tava samun karvuwa ba.
Don haka, ya yi kira ga gwamnati da ta gurfanar da duk wadanda suka taka rawa wajen cin zarafin al’umma tare da tabbatar da adalci.
Sanusi Isa, daraktan kungiyar ‘Amnesty International’ ta kasa, shi ma ya yi magana makwatankwaciyar wannan, inda ya yi nuni da cewa, duk wadanda suka aikata laifuka; su fuskanci hukunci na gaskiya.
Sannan ya kara da cewa, dukkanin wadanda abin ya shafa da wadanda suka tsira da iyalansu, sun cancanci a yi musu adalci.
daya daga cikin Shugabannin al’ummar Chibok, Mutah Nkeki, ya bayyana ra’ayinsa a matsayin rashin adalci da gwamnati ta shirya a kan ‘yan asalin Chibok da sauran daukacin wadanda ta’addancin ya shafa.
Ya yi zargin cewa, ‘yan matan makarantar Chibok da Boko Haram suka sace a shekarar 2014, an hana su ganawa da shugabanni da kuma iyayensu, tun bayan da suka tsere daga hannunsu.
Har ila yau, ya kara da cewa, babban abin takaicin shi ne, faruwar lamarin ya jawo mutuwar iyaye dama, inda y ace wadanda ke raye; ba a bas u damar ganin ‘ya’yansu mata da suka kuvuta ko aka kuvutar da su ba.
Da aka tuntuvi kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na Jihar Borno, Farfesa Usman Tar; ya musanta dukkanin zarge-zargen.
Ya ce, savanin zargin da ake yi; gwamnati jihar ta bayar da makudan kudade, domin sake tsugunar da al’umma.