Masana kimiyyar kasar Sin sun kirkiro wani sabon samfurin kirkirarriyar basira ta fasahar AI domin yin hasashen zuwan mahaukaciyar guguwa, wanda hakan ya ba da sabuwar fa’ida da kara haskaka hanyoyin inganta shirin tunkarar bala’o’i a duniya.
A kwanan baya, masu bincike daga cibiyar nazarin teku a kwalejin kimiyya ta kasar Sin sun wallafa wannan binciken a cikin mujallar da ke wallafa harkokin kimiyya ta kasar Amurka, watau “Proceedings of the National Academy of Sciences.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)